Daga Imrana Abdullahi
Hajiya (Dr) Maryam Sani Abacha, Uwargidan tsohon shugaban Nijeriya, Marigayi Sani Abacha ta jajantawa al’ummar Maiduguri bisa ibtila’in ambaliyar ruwa da aka samu. Inda ta yi kira ga al’ummar Nijeriya da su tallafawa al’ummar Maiduguri da duk abin da Allah ya hore musu domin rage musu radadi.
Maryam Abacha ta soma da cewa, “ina jaje ga Nijeriya baki daya. Ina jaje ma al’ummar Borno. Borno gari na ne kuma mutane na ne. Iyayena duka daga Borno suke”, ta lurantar.
Ta ci gaba da cewa, “Kuma magana da yawa da dangin mamana. Ko da safen nan mun yi magana kan yadda za a canza musu muhalli saboda Unguwarsu ruwa ya cinye. Da kuma yadda za a tallafa a kan abinci da kudi da sauran su. Da ni da yarana mun zauna akan abubuwan da mu ma za mu tallafa ma mutanen Maiduguri. Ta yadda inda kowa ya kawo kadan-kadan za a samu a yawa”, ta nusasshe.
Ta kara da cewa; “ina jaje na wannan ambaliyar ruwa. Lokacin maigida an yi irin wannan ambaliyar ruwa, kuma ya bayar da taimako. Yanzu wajen shekara 30 ke nan”.
Hajiya Maryam Abacha ta yi kira da a yi kokarin gyara wannan dam din domin kaucewa aukuwar hakan a gaba, inda ta ce; “ya kamata a yi kokari a gyara wannan dam din. Saboda gobe ka da ya auku haka nan. Mu kasarmu gaskiya muna da sakaci, muna da kunci”.
Ta nemi da kowa ya zo ya bayar da na shi tallafin da taimako; “duk abin da za a taimaki al’umma a yi, a rika taimako. Ubangiji Allah ya kare gaba. Allah yasa kaffara a gare su mutanen Maiduguri. Allah yasa wannan ruwa ya zama alheri. Allah yasa ya wanke wannan jinin da Boko Haram suka zubar a Maiduguri.
Hajiya Maryam ta karkare da cewa; “ina kira ga ‘yan Nijeriya kowa ya kawo dauki, da mai yawa da kadan. Da kadan-kadan sai ya yi yawa, a kawo mutanen Maiduguri dauki. Allah ya taimaki Nijeriya.”