Ina Da Yakinin Tambuwal Zai Kawo Gagarumin Ci Gaba A Yankinsa – Atiku Yab
Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Atiku Muhammad Yabo, fitaccen dan siyasa ne da kowa ya sanshi a duk fadin Jihar Sakkwato kasancewarsa mutum ne mai kishin al’umma, ya bayyana cewa ya na da yakinin tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Sanata Aminu Waziri Tambuwal zai kawo gagarumin ci gaba a yankinsa, Jiha da kasa baki daya.
Dan gwagwarmayar siyasar Alhaji Atiku Muhammad Yabo, ya taya tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Kuma Sanata Mai ci a halin yanzu Alhaji Aminu Waziri Tambuwal murnar rantsar da shi da aka yi, a matsayin Sanata daga Jihar Sakkwato
Alhaji Atiku Yabo ya bayyana tabbacin cewa, tsohon Gwamnan zai kawo gagarumin ci gaba a yankin da yake wakilta da kuma Jihar Sokoto baki daya, musamman ta la’akari da dumbin ayyukan ci gaba da ya shimfida a lokacin da yana Gwamna a Jihar.
Ya ce “Majalisa ta Goma, za ta kasance daya daga cikin majalisun da suka yi fice, musamman irin yadda aka samu tsohon Gwamnan a cikin ta”.
“Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kasance jajirtacce ne, Mai dagewa, ga son talakawa, Kuma tabbas zai kawo ci gaban da ba’a tsammani a yankin da yake yi wa wakilta, kai har ma da Jihar Sakkwato baki daya”, Alhaji Atiku Yabo.