Home / Garkuwa / Ina Neman Hakki Na Ne A Gaban Kotu – Musa Gashash

Ina Neman Hakki Na Ne A Gaban Kotu – Musa Gashash

Daga  Imrana Kaduna

Sardaunan matasan Nijeriya Alhaji Mohammed Ibrahim Musa Gashas ya maka rundunar Sojin Nijeriya a gaban babbar Kotun Tarayya da ke da zamanta a Kaduna yana neman hakkinsa

Mai Shari’a Alkaliyar babbar Kotun tarayya  Z. B Abubakar, ta karatu karar a lokacin wani zaman kotun da aka yi a ranar Jiya Talata.

Da yake tattauna  da manema labarai jim kadan bayan fitowa daga Kotun, Mohammed Gashash ya ce,” Sojojin sun kama ni sun kuma  tsare ni ba tare da wata kwakkwarar hujja ba kuma ba tare da sun gabatar dani a gaban Kotu ba.”

Ya ci gaba da cewa, ” sun kama ni a ranar daya ga watan Janairun shekarar 2020, lokacin da suka zo gida na da misalin karfe hudu na dare sannan kuma suka ce za su binciki gida na.”

A cewar Gashash, na tambaye su sun zo da takardar da za su kama ni, suka ce, a’a, na kuma tambaye su, ko sun zo da takardar da ta ba su umarnin su yi bincike a gida na, suka ce, a’a.

Ya bayyana  cewa, sojojin a cikin kakin su sun cire sunayen su wanda wannan ba daidai ba ne, inda ya kara da cewa, ” nace masu ba zan fita daga gida na ba a cikin wannan daren sai dai su bari da rana ido na ganin ido”.

Ya sanar da cewa, sun kuma kara dawowa gidan shi bayan kwanuka goma suka kewaye gidan har na tsawon kwanuka shida.

Alhaji Mohammed Ibrahim Musa Gashash ya bayyana cewa, zaman na Kotu na yau, an gabatar da karar ne a gaban babbar Kotun ta Tarayya da ke zamanta a Kaduna.

Shi kuwa lauyan mai kare wanda ya shigar da karar a gaban babbar Kotun ta Tarayya Barista Sani Malam Garba ya ce, yau an fara sauraron karar da wanda ya ke karewa Alhaji Mohammed Ibrahim Musa Gashash ya shigar a kan rundunar Sojin kan tauye masa ‘yancin sa kuma Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Fabirairun shekarar 2020.

A ranar 24 ha watan Fabrairu, 2020 ne za a ci gaba da shari’ar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.