Home / Labarai / Ina Son A Kaini Kara Kotu – Mahadi Shehu

Ina Son A Kaini Kara Kotu – Mahadi Shehu

Imrana Abdullahi
Fitaccen dan kasuwa Alhaji Mahadi Shehu ya yi kira ga dukkan wanda yake gani ya fadi wani ABU dangane da badakalar kudin da ake yi a Jihar katsina bai gane ba da ya kai shi kara kotu domin a bi masa hakki a kotu.
Mahadi Shehu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta rediyon freedom mai gajeren zango a kaduna.
“Duk wanda yake gani na yi magana ko zamba ko abin da bai dace ba amma bai kai ni kara ba, ban yafe ba, domin wannan abin da nake yi ija ba ce domin jama’a na ta fatar samun dauki daga Allah shin yaushe nasara za ta zo taimako dag madaukaki, bisa haka lallai taimako daga Allah na nan zuwa”.
Ya ce dukkan wanda bai gane ba da irin abin da ake fadi dangane da batun kudi a Gwamnatin Katsina mai ci yanzu, in ba a kai ni kara ba ban yafe ba.
Ana badakalar kudi sosai a Jihar katsina, ina kudin da aka bari na gado daga Gwamnatin Ibrahim Shehu Shema?
“A yanzu babu sauran kaddarar Gwamnati a Jihar Katsina duk sun sayar da su duk baki daya, kuma batun Gwamnatin baya ta Shema in ka hada ta da wannan Gwamnatin, ai shi Barista Ibrahim Shehu Shema sahabi ne a kan wannan Gwamnatin da ke ci a katsina”.
Mahadi ya kara da cewa ta yuwu irin yadda jama’a suka yi addu’o’I ne da watan Azumi na Allah ya kawo masu dauki yasa gani na fito ina yin bayani filla filla ga yadda badakalar kudi take a Jihar katsina.
Mahadi ya kuma tabbatar da cewa an shiga firgici a Gwamnatin Jihar katsina, wanda sakamakon hakan aka mikawa majalisar Jihar Katsina wata doka mai kama da almajir da za ta rataye wuyan ma aikatan Jihar Katsina bayan sun ajiye aiki suna neman kudin sallama da na fansho.
Ya kuma ce an kira Malamai, sarakun, Hakimai da Dagatai taro a gidan Gwamnati amma aka ce masu ana son yin shawara ne kan yadda za a bude Islamiyyoyin Jihar katsina, ” ina da dukkan hoton mutanen da suka je wajen wannan taro da sunayensu kaf baki daya.
Mahadi ya kuma sha alwashin cewa idan an bashi dama zai bayyana wa duniya irin kudin da Gwamnatin Jihar Katsina ta samu daga Gwamnatin tarayya da na taimakon da aka samu da yawan abin da ake biyan ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi Albashi da kuma irin bashin da Gwamnatin Masari ta rungumowa mutanen Jihar Katsina da dai wasu al’amuran kudi da yawa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.