Home / News / JAM’IYYAR LEBO ZA TA KADDAMAR DA NEMAN ZABE A RANAR 6 GA WATAN FABRAIRU

JAM’IYYAR LEBO ZA TA KADDAMAR DA NEMAN ZABE A RANAR 6 GA WATAN FABRAIRU

Za Mu Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Kananan Hukumomi A Sabon Gari

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Jam’iyyar Lebo ta kasa reshen Jihar Kaduna ta bayyana cewa za su kaddamar da Yakin neman zaben kananan hukumomi a ranar Litinin 6 ga watan Fabrairu domin shiga sako da dukkan lungunan Jihar Kaduna su nemo goyon bayan jama’a.

Kuma za a yi taron gangamin ne a Sabon Garin Zariya da ke karamar hukumar Sabon Gari a cikin Jihar Kaduna.

Sun bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da suka kira a dakin taro na babban ofishin dan takarar Gwamna Mista Jonathan Asake a cikin garin Kaduna.

Darakta Janar na Yakin neman zaben Tsahiru Bako ya tabbatarwa da jama’ar Jihar Kaduna cewa idan sun bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga jam’iyyar Lebo da yan takararta baki daya ba za su yi da na Sani ba sam.

Tshiru Bako ya ci gaba da bayanin cewa “Batun katin zabe ne ya bamu karfin Gwiwa cewa za mu lashe zabe domin samar da sabuwar Najeriya”.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron manema labaran, Shugaban jam’iyyar Lebo na Jihar Kaduna Alhaji Auwal Ali Tafoki, ya ce su ba za su yi amfani da yan bangar siyasa ba domin biya wa kansu bukata, sai dai ayi kira tare da fadakarwa ga jama’a su samu goyon baya da hadin kai su kuma yi amfani da katunan zaben su

Kamar yadda yake a cikin manufar Yakin neman zaben mu cewa za mu tabbatar da ilimi, tsaron al’umma da inganta tattalin arziki a Jihar Kaduna

“Hakika muna da dabarun neman zabe wanda hakan ya sa muka ce za mu fara gangamin Yakin neman zabe daga garin Sabon Gari a karamar hukumar Sabon gari domin mun san hakika jama’a na tare da jam’iyyar mu tare da yan takararmu baki daya.

Dan takarar mataimakin Gwamna ya tsaya zabubbuka da yawa ya kuma yi nasara har ya zama shugaban masu rinjaye a Jihar Kaduna kuma ya zama kwamishina a Jihar da sauran mukamai da yawa

Hakazalika shi ma dan takarar Gwamna kansa ya tsaya takara ya zama dan majalisar tarayya ta kasa ya zama mai bayar da shawara ga shugaban kasa na can baya Jonathan, kima ga shi tsohon Malamin makaranta da ya san harkar ilimi ciki da bayan ta

” masani ne a kan ilimin sanin zuwa sararin samaniya don haka mu yan takarar mu lafiya kalau za su iya aikin da za a ba su da ikon Allah

“Hakika dan takarar shugaban kasa Peter Obi ya ga abin al’ajabi a Kudancin Kaduna domin ya ga yawan jama’ar da suka taru a wurin

Kuma dan takarar Gwamnan Lebo Jonathan Asake mutum ne da ya tashi a cikin jama’a don haka ya san abin da jama’ar ke ciki kuma zai yi bakin kokarinsa wajen magance matsalar.

Kuma Jonathan Asake bashi da kabilancin yare ko addini mutum ne mai son jama’a da taimakon Juna a koda yaushe.

Zamu yi Yakin neman zabe ne ta hanyar zuwa Gida Gida, taron gangamin jama’a da kuma taron jama’a a muhimman wurare daban daban

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.