Home / Kasuwanci / Jihar Taraba Na Kan Gaba Wajen Ma’adinai – Yusu Tanimu Njeke

Jihar Taraba Na Kan Gaba Wajen Ma’adinai – Yusu Tanimu Njeke

Mustapha Imrana Abdullahi
An bayyana Jihar Taraba a matsayin Jihar da ke kan gaba wajen zaman lafiya da kuma ma’adanan karkashin kasa.
Kwamishinan ciniki da masana’antu na Jihar Taraba Honarabul Yusuf Tanimu Njeke ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a rumfar Jihar Taraba a kasuwar duniyar kasa da kasa da ke Kaduna a Nijeriya.
A hagu kwamishina Yusuf Tanimu Njeke tare da babban sakataren ma aikatar lokacin da yake ganawa da manema labarai a kasuwar duniya ta kaduna
Honarabul Yusuf Tanimu ya shaidawa manema Labaran cewa batun nan da ake yi cewa Gwamnan Taraba na yi na ku bani zaman lafiya in yi maku aiki, domin a samu ingantaccen ci gaban da kowa ke bukata.
Honarabul Yusuf Tanimu ya ci gaba da cewa shi da kansa ya zagaya kasuwar duniya ta kasa da kasa da ke ci a Kaduna inda ya kaga abubuwa da dama daga kasashen duniya daban daban.
Rumfar Jihar Taraba kenan a kasuwar duniyar kasa da kasa ta kaduna
“Naga mutanen kasashen waje irinsu Egypt wato Misra da sauran kassshe sun zo tare da kayayyakin gargajiyarsu da sauran kaya da yawa abin sha’awa kwarai”.
Honarabul Tanimu ya bayyana zaman lafiyan da aka samu a Taraba da cewa ya samu ne sakamakon irin kwazon Gwamnan Taraba na yanzu inda yake aiki ba dare ba rana domin tabbatar da zaman lafiyan da ya haifar da ci gaban Jihar, arewaci da kasa baki daya.
Jihar Taraba na da arzikin Katako inda ake sarrafa shi wajen yin abubuwa daban daban har da kwanukan cin abinci kamar yadda zaku gani a wannan hoton
“Muna kira ga daukacin al’ummar duniya da su zo Jihar Taraba su zuba jari da fuskar masana’antu, ma’adinai, aikin Noma, cinikayya, otal da yawon shakatawa da sauran fannonin rayuwa baki daya, kasancewar Gwamnatin Jihar Taraba a shirye take domin hada gwiwar da duk masu bukatar hakan”.
Ga irin kayan ma’adinai da kayan gargajiyar da al’ummar Taraba ke samarwa kamar yadda suka kawo su a kasuwar duniya ta kaduna
Ya kara da cewa a halin yanzu babu wata damuwa a Jihar Taraba don haka kowa zai iya zuwa domin inganta al’amuran kasuwanci baki daya.
Kwamishinan ya kuma bayyana irin nasarorin da suka samu a shugabancin Jihar inda ya ce a ma’aikatarsa sun samar da filin da dukkan mai son yin wata masana’anta zai iya zuwa domin gina masana’antar da yake bukata.
Ga irin kayan da masana’antu Jihar Taraba ke samarwa da suka hada da Shinkafa,Ganyen shayi, Manja da sauransu
Ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar Jihar da su ci gaba da zaman lafiya da Junansu ta yadda Gwamnan Jihar zai samu zarafin aiwatar da aiki domin ci gaban jama’a.
Ga irin arzikin Katakon da Jihar Taraba ke da shi

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.