Home / Kasuwanci / Kamfanin Dangote Na Samar Da Damar Zuba Jari Da Yawa A Afirka

Kamfanin Dangote Na Samar Da Damar Zuba Jari Da Yawa A Afirka

Kamfanin Dangote Ya Samu Lambar Karramawa A Kasuwar Duniya Ta Kaduna

 

 

KATAFAREN Kamfanin Dangote da ya mamaye daukacin Nahiyar Afirka ya shahara wajen kokarin sama wa dimbin jama’a damar zuba jari a fannonin kasuwanci da kuma ayyukan taimakawa rayuwar jama’ar duniya baki daya.

 

Wannan shi ne ainihin matsayar da aka cimma, kasancewar hakan lamari ne na zahiri a babban taron baje kolin kasuwar duniyar kasa da kasa karo na 44 da aka kammala a wannan shekarar 2023 a Kaduna.

 

Kamfanin na Dangote ya kuma samu babbar lambar karramawa da ta fi ta kowa a cikin jerin wadanda suka halarci taron na kasuwar baje kolin kayayyakin kamfanoni da masana’antu, da ya gudanar a harabar filin kasuwar da ke Rigachikun, kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

 

Da yake tattaunawa da manema labarai a ranar bikin kamfanin Dangote a kasuwar duniya ta Kaduna, Farfesa masanin tattalin arziki, Umar Dantsoho, cewa ya yi Kamfanin Dangote ya shahara kwarai wajen samawa jama’a abin yi da kuma ba su damar samun damarmaki da yawa a fannin zuba jari a Najeriya da nahiyar Afirka baki daya.

Ya bayyana kamfanin Dangote a matsayin wanda ya shahara a wajen ciyar da nahiyar Afirka gaba, wanda daman abin da kamfanin ya Sanya wa gaba kenan.

 

A kwanan, kamfanin Dangote Sanya hannu a wata yarjejeniyar samar da tan miliya shida a shekara da kamfanin kasa da kasa Sinoma a kasar Cina wanda hakan zai taimaka wajen karin samar da kayayyaki a Najeriya da Afirka a samu tan miliyan 57.6 a shekara.

 

Ban da Gwamnati, kamfanin Dangote ne ke sama wa jama’a aikin yi a Najeriya.

Da yake gabatar da nasa jawabin mataimakin shugaban na biyu a  kasuwar duniyar kasa da kasa (KADCCIMA). Alhaji Faruk Suleiman, ya jinjinawa kamfanin a kan irin yadda yake kokarin samar da ayyuka a nahiyar Afirka, ya kara da cewa matatar albarkatun mai ta Dangote za ta canza fuska da duk yanayin tattalin arzikin Afirka baki daya.

 

Janaral manaja, mai kula da Sayarwa da tallar kayan kamfanin Sukari na Dangote mai kula da yankin Arewa maso Yamma, Alhaji Abdulsalam Waya,cewa ya yi kamfanin zai ci gaba da sama wa jama’a dama ga duk dan Najeriya da ke son zuba jari a matsayin mai sayar da kayan kamfanin Dangote ko kuma ya zuba jari a babbar kasuwar.

 

Ya kara da cewa, taken kasuwar na Bana: karawa kaya inganci domin samun ci gaba, hakika ya yi dai dai, saboda kamfanin Sumunti na Dangote na fitar da kayansa zuwa kasashen Afirka da dama, wanda hakan ke Sama wa dimbin jama’a aikin yi da kuma dama a dukkan fannonin rayuwa baki daya.

 

Kamfanin Dangote ne ke kan gaba wajen daukar nauyin shirya kasuwar duniya ta Kaduna karo na 44.

Da yake gabatar da nasa jawabin shugaban Kasuwar Alhaji Suleiman Aliyu bayyana hadin Gwiwar da ake yi da kamfanin Dangote a matsayin wani abu mai amfani musamman ta fuskar ci gaban harkokin kasuwanci a Najeriya.

 

Ya ce irin taimakon da kamfanin Dangote ke yi a wajen shirya wannan kasuwa ba zai misaltu ba.

Da yake tattaunawa da manema labarai, Darakta Janar na kasuwar Malam Usman Saulawa cewa ya yi kamfanin Dangote ne wanda ya fi kowa taimakawa wajen shirya wannan kasuwar kuma sun dade suna yin hakan a duk shekara.

 

Ya ce, “Kamfanin Dangote ne ke taka rawar mai matukar goyon baya da kuma hada Gwiwa wajen shirya wannan kasuwar tsawon shekaru da dama. Kuma yadda yake halartar kasuwar na kara kwarjini da martabar kasuwar”.

 

Darakta Janar din ya bayyana kasuwar ta Bana a matsayin wani abin sha’awa domin akwai babban taron yan kasuwa domin tattaunawa a tsakanin Juna, wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci musamman ga mahalarta kasuwar.

 

Kamfanonin da suka halarci kasuwar ta Bana a karkashin kamfanin Dangote sun hada da Kamfanin Sumunti, Kamfanin Sukari,NASCON,Kamfanin Takin Zamani da kuma kamfanin harhada motoci na Sinotruk (West Africa Limited).

 

A cikin wata takardar da ta fito daga bangaren yada labarai na kamfanin Dangote ta ce duk wani wanda ya halarci wannan kasuwa da ke son yin hulda da duk wani kamfanin da ke karkashin kamfanin Dangote zai iya samun damar yin hakan ta hanyar zuwa wani bangaren musamman da aka ware a rumfar kamfanin a kasuwar duniya ta kasa da kasa a Kaduna.

 

Ta bayyana Kaduna a matsayin wata babbar Kasuwa a Najeriya, inda suka ce idan an yi la’akari da matsayin tarihin siyasa cewa nan ne cibiyar arewacin Najeriya.

 

 

Daga, Yagana Ali, Yola.

About andiya

Check Also

Samar Da Tsaro Sai Kowa Ya Bayar Da Gudunmawarsa – Kaftin Joji

….A koma ga masu unguwanni, dagatai da hakimai Kaftin Muhammad Joji ya bayyana cewa lallai …

Leave a Reply

Your email address will not be published.