Home / Kasuwanci / Kamfanin Google Zai Taimakawa Jaridun Yanar Gizo 16

Kamfanin Google Zai Taimakawa Jaridun Yanar Gizo 16

 Imrana Abdullahi

Kamfanin yanar Gizo na Google a karkashin sharinsa na Labaran Google Initiative, ya bayyana cewa zai taimakawa wadansu jaridun yanar Gizo guda Goma 16 da suke a tarayyar Nijeriya da suka hada da shahararriyar Jaridar Daily Nigerian da kudi.

Ludovic Blecher, shi ne shugaban bangaren  labaran Google, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa cewa JERF sun tanaji kudi dala miliyan 39.5 domin taimakawa masu wallafa jaridu a kasashe 115 a wasu watanni da duka gabata.

Kamfanin Dillancin labaran Nijeriya ya ruwaito cewa shirin da aka kaddamar a watan Afrilu, an yi shi ne sa nufin taimakawa wasu kamfanonin jaridu da suka fuskantar matsalar kudi sakamakon karancin samun tallace tallace.

Wanda ya fitar da sanarwar ya ci gaba da bayanin cewa jaridun da za a taimakawa sun hada da Aledah.com,City Mirror News, Daily Nigerian, News Wire NGR, Lagos Post Media, News feed Nigeria, Premium Times

Sauran sun hada da Sundiata Post, Sunrise NewsPaper, Tell Magazine, Daily Times, Daily Report, Eagle Online, The Median, TNG da kuma jaridar Punch da suka hada da Punch ta ranar Asabar da Lahadi da kuma jaridar Punch ta yanar Gizo.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.