Home / Kasuwanci / Kamfanin Sumunti Na Dangote Sun Karyata Batun Farashin Garabasa

Kamfanin Sumunti Na Dangote Sun Karyata Batun Farashin Garabasa

…Kuma a halin yanzu Suna Kokarin binciko wadanda suka kitsa maganar, su kuma kai su gaban shari’a a kan laifin  karyar da suka yada.
Shugabannin gudanarwar kamfanin Sumunti na Dangote sun Karyata wani labarin da ake yadawa a wadansu kafafen jaridun yanar Gizo cewa wai sun koma sayar da kayan nasu a kan farashin garabasa kuma sun canza farashi.
A matsayin mayar da martani a kan rahotannin karkatar da jama’a, babban jami’in kula da kaya da kuma sadarwa na kamfanin Dangote baki daya, Anthony Chiejina ya bayyana rahoton karyar da aka yada a matsayin wani kokarin yin batanci da haifarwa da kamfanin matsala a kan batun karya da wasu suka yada.
Ya kara da cewa hukumar gudanarwar kamfanin Dangote tuni har sun sanar da jami’an tsaro domin nemo wadanda suka kitsa wannan maganar, su samo sunansu da nufin kunyatar da su  da wadanda suka aikata hakan da nufin yaudarar jama’a ta hanyar yada bayanan karya da yaudarar al’umma.
Sai ya bayar da shawara ga masu sayan Sumuntin Dangote da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da sayan ingantaccen Sumuntin da ke dauke da sanannen tambari da aka Sani kuma su yi hankali da yan yaudara da yan damfara, da ka iya samun damar karbar wa jama’a kudi ta hanyar yaudara.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.