…muna murnar samun tashar Jiragen ruwa ta kan tudu a Fintuwa
Wani dan kasuwa kuma dan kishin kasa Alhaji Lawal Yaro Manajan A A Albasu ya bayyana samun tashar Jiragen ruwa ta kan tudu da aka samu a Funtuwa a matsayin wani gagarumin ci gaban da zai taimakawa Jihar Katsina da kasa baki daya a matsayin Funtuwa na wani wurin da ke da albarkar kasar Noma da ta fi ta ko’ina kyau.
Lawal Yaro Manaja ya bayyana hakan ne a lokacin da ya halarci taron kaddamar da tashar Jiragen ruwa ta kan tudu a garin Funtuwa a matsayin wakilin mai gidansa AA Albasu.
Lawal Manaja ya ci gaba da bayanin cewa hakika jama’a baki daya suna cike da gagarumin farin cikin da ba za a iya misalta shi ba a cikin dan kankanin lokaci ba.
Yaro Manaja ya ce a halin yanzu a matsayinsu na kananan da kuma har ma da manyan yan kasuwa sun samu cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali idan sun je duk wata kasa kamar Cina,Dubai wato tarayyar kasashen Larabawa da sauran kasashen duniya ba su da wata damuwa domin kuwa sun san kayan da suka yi oda kawai garin Funtuwa za su zo ba tare da wata damuwa ko kokwantoba, don haka muna kara yi wa Allah godiya da wannan ni’imar da ya yi wa Funtuwa,Jihar katsina da kasa baki daya”.
Kamar yadda kowa ya Sani ” yankin Funtuwa na da kyakkyawar ingantacciyar kasa mai dimbin albarka da babu irin ta a fadin Najeriya domin an gyada an tabbatar da cewa duk abin da aka shuka za a iya samunsa kamar yadda ake bukata don haka samun wannan tashar ta Jiragen ruwa ta kan tudu wata karin albarka ce da ta samu Funtuwa da kasa baki daya, musamman ga yan kasuwar daukacin arewacin Najeriya baki daya”.