Home / KUNGIYOYI / KATIN ZABE NE ZAI KAREWA MA’AIKATA MUTUNCINSU – AYUBA MAGAJI SULEIMAN

KATIN ZABE NE ZAI KAREWA MA’AIKATA MUTUNCINSU – AYUBA MAGAJI SULEIMAN

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, shugaban kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) reshen Jihar kaduna  ya yi kira ga daukacin ma’aikata da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin tabbatar da yin katin Jefa kuri’a da zai ba su damar zaben shugabannin da za su jagorance su a kowane irin mataki.
Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Kaduna.
Ayuba Magaji ya ce a matsayinsa na shugaban kungiyar Kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna ya na fadakar da ma’aikata da su tabbatar sun bi wannan hanyar ta yin rajistar zabe domin ita ce mafita ga kowa.
” Duk wanda bashi da katin yaje ya tabbata ya yi, wanda nasa ya bace ya yi sabo, wanda kuma ya canza gari ko wurin zama duk kowa ya tabbatar ya mallaki katin, kuma ga duk wadanda suke da shi a sama wa katin ma’ajiya mai kyau a tabbatar an adana shi sossi”.
” Mu a matsayin mu na ma’aikata muna bukatar Gwamnatin da za ta kula da mutuncin mu da na iyalin mu baki daya musamman ta fuskar kare hakkin mu a koda yaushe, saboda haka wannan kira ne da yake da muhimmanci ya kuma zama wajibi mu shugabanni mu gaya wa ma’aikata su san cewa yancinsu, Darajarsu da mutincinsu da mutuncin aikinsu da na iyalansu ya na da alaka da wannan katin”.
Saboda ko ba komai mun san meke faruwa a Jihar mu da haka kawai ka na zaune sai ace ga wani dalili haka kawai ace sai ka na da kaza ko baka da kaza da kaza idan baka da shi a cure ka aiki duk da baka shirya ba baka tanaji komai ba kuma baka iya komai ba, don haka hakika abu ne mai matukar muhimmanci kwarai da gaske.
” Domin shi ne darajarka, iyalinka saboda da aikin nan ne muke ciyar da iyalin mu da daukar nauyin su saboda haka ina kira ga duk ma’aikaci idan ya na da katin zabe ya saya masa alabe na ajiya ki kuma ya saya wa katin asusun ajiya na musamman, idan ma mutum na son canza inda zai yi zabe ayi Sauri aje aji kamar yadda ita hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana domin ana tunanin zuwa karshen wadannan za a rufe.
Ina kara jaddadawa ma’aikata cewa idan ranar zabe ta zo kowa ya kare mutincinsa da na aikinsa da iyalansa baki daya  wannan shi ne kiran da muke yi kawai.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.