Home / News / Sakamakon Zaben Osun Manuniya Ce Ga APC – Inji Dokta Ayu

Sakamakon Zaben Osun Manuniya Ce Ga APC – Inji Dokta Ayu

Daga IMRANA ABDULLAHI Kaduna
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Dokta Iyorchia Ayu ya bayyana farin cikinsa da irin yadda al’ummar Jihar Osun suka fito kwansu da kwarkwatarsu baki daya suka ba jam’iyyar PDP hadin kai da goyon baya wanda sakamakon hakan suka samu gagarumar nasara.
Dokta Iyorchia Ayu, ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar da ke dauke da da hannunsa da aka rabawa manema labarai.
Takardar ta yi bayanin cewa a yau ranar 16 ga watan Yuli, mutanen Jihar Osun suka fita fagen yin zabe kuma har sun zabi Gwamnan da suke bukata
Kuma a yan awoyin da suka gabata jami’an hukumar zabe na kasa mai zaman kanta sun bayyana dan takarar jam’iyyar PDP Sanata Ademola Nurudeen Jackson Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben.
Takardar ta ci gaba da bayanin cewa duk da kokarin da Gwamnan APC Adegboyega Oyetola da Jam’iyyarsa ta APC suka yi na domin ganin sun kawo mana cikas game da batun nasarar da muka yi.
Sai dai muka yi amfani da ofishin jam’iyya na Jiha. Domin ba mu da damar samun filin wasan da ya dace mu yi amfani da shi, amma kuma mu na cikin zuciyar jama’a, ta fuskar goyon baya da kuri’u.
Tazarar yawan kuri’a da ke 403,371 sabanin Gwamna mai ci da ya samu kuri’a 375,027 wannan babbar mqnuniya ce da ke tabbatar da samun nasara.
Shekaru 12 da sula gabata musamman ma a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2010, jam’iyyar PDP ta yi rashin nasarar lashe zaben Jihar Osun ba kuma ta hanyar zabe ba a’a ta hanyar shari’a.
Tun a wancan lokacin Jihar Osun ta kasance a cikin wani mawuyacin hali musamman ta fuskar rashin ci gaba.
Shekaru hudu da suka gabata, PDP ta lashe zaben Gwamna, amma aka yi wa dan takarar mu fashin kuri’a da rana tsak, Sai muka koma baya domin duba lamarin sosai kuma a yau ga shi mun sake samun nasara.
Saboda haka kamar yadda takardar da yi bayanin cewa a yau ba wai ranar yin murna a kan murna bace kawai, ta zama wata rana ce ta shakar yanci. Domin PDP ta sake dawowa kan karagar mulki a Jihar Osun, an yi waje da masu fadi ba cikawa.
“Ina ta ya mutumin da ya samu nasara har sai biyu, wato shi ne Adeleke, Ina kuma ta ya murna ga mutanen Jihar Osun da duk masu zama a Jihar. Ina yi wa kowa jinjina musamman ma masu ruwa da tsaki da suka kasance tare da mu ta hanyar aiki, addu’o’i da kuma kyautata zaton samun nasara.
Kun amince da jam’iyyar PDP. Kun ki bari a yi maku barazana. Kun ki bari wani ya saye ku da kayan abinci da kuma yan sulalla. Kun ki bari ayi amfani da ku ta yin bangar siyasa. Hakika kun yi abin da ya dace.
Ayu ya ce ya na yin godiya ga babban kwamitin fafutukar neman zabe na zaben Gwamnan PDP na Jihar Osun wanda ke karkashin jagorancin Gwamna Duoye Diri, bisa iron kokarin da suka yi. Na kuma yi godiya ga dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP Gwamna Arthur Ifeanyi Okowa bisa aikin da ya yi tukuru. PDP na murna da farin ciki da ku baki daya.
“Kun taimaka kun dawo da PDP kan madafun iko bayan shekaru 12. Don haka kun dawowa jama’a irin abin da suke tunani da ke karfafa Gwiwa. Amma kuma ban da hakan, kun kuma sabunta umarnin gaggawa cewa Gwamnatin APC ta tattara ina ta ina ta.PDP ta bayar da umarni ta hanyar bayar da umarnin gaggawa a watan Disamba shekarar da ta gabata lokacin da wannan shugabancin ya shiga ofis.
Takardar Ayu, ta kara bayanin cewa wannan zaben raba gardama ne da ke yin manuniya ga jam’iyyar APC, kuma hakan na bayar da tabbacin cewa yan Najeriya na son ganin jam’iyyar PDP ta dawo. Saboda haka PDP na dawowa!
Na yaba tare da jinjinawa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da kuma jami’an tsaro da suka taka rawar yan baruwanmu a lamarin zaben wanda hakan ya Sanya sai da aka kidaya kuri’un da aka kada.
Iyorchia Ayu, ya ce a halin yanzu babban abin da ke gaban su shi ne canzawa daga yan adawa zuwa masu rike da madafun iko. Wannan ne abin da za a yi a yanzu.
Ayu, ya kara da cewa ya na yin kira ga daukacin yayan jam’iyyar PDP da kuma dukkan yan Najeriya da su rungumi Jirgin tsira na jam’iyyar PDP. Kada wani ko wasu su bari a bar su a baya.Domin inda muka tunkara shi ne fadar shugaban kasa ASO VILLA.
“Da jam’iyyar PDP,” Najeriya za ta ci gaba da bunkasa, kai tuni ma har ta tumbatsa.domin jama’ar Jihar Osun sun yi magana.saboda haka sauran yan Najeriya ma yakamata su yi magana, da babbar murya a ranar 25, ha watan Fabrairu 2023 mai zuwa.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.