Home / News / KO A TARON SHUGABAN KASA NE SAI HAKA – Isyaku Wada Faskari

KO A TARON SHUGABAN KASA NE SAI HAKA – Isyaku Wada Faskari

 

DAGA IMRANA ABDULLAHI
An bayyana irin gagarumin taron tarbar dan takarar Gwannan Jihar Katsina karkashin APC Dokta Dikko Umar Radda da cewa taron ko shugaban kasa ya zo garin Funtuwa da ke Jihar Katsina idan aka yi masa wannan gangamin hakika sai haka.
Kwamared Isyaku Wada Faskari ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da wakilin mu ya wayar Salula.
Kwamared Isyaku Wada Faskari ya ce hakika sun Gamsu da irin karamcin da mutane  Funtuwa suka yi masu, domin sun Karrama dan takarar Gwamnan Jihar Katsina tare da dukkan mutanen da ke tawagarsa.
“Muna murna da farin cikin abin da muka gani a karamar hukumar Funtuwa domin an Karrama yayan APC manyansu da kananansu da dukkan mambobin jam’iyyar don haka ba za mu mance da irin wannan karamcin ba, kuma da zarar Allah ya ba APC nasara a zabe mai zuwa hakika za a sakawa dukkan jama’ar Jihar Katsina da abin alkairi”.

Sai ya yi kira ga daukacin masu katin Jefa kuri’a tun daga mazabun Jihar Katsina zuwa matakin Jiha da na kasa baki daya da su tabbata sun zabi jam’iyyar APC domin ta na da kishin al’ummar kasa a dukkan tsare tsaren ta, “zaben APC shi ake cewa sayen nagari mayar da kudi guda, don haka Talakawa su gujewa masu romon baka”.

About andiya

Check Also

The Daily Hug For Appreciation 2023

The daily hug for 28/11/23 is this appreciation of an echo shared by my dear …

Leave a Reply

Your email address will not be published.