Home / KUNGIYOYI / KOTU TA BUKACI TSOFFIN KANSILOLIN YOBE 172 SU BAYYANA A GABAN TA A BAUCHI

KOTU TA BUKACI TSOFFIN KANSILOLIN YOBE 172 SU BAYYANA A GABAN TA A BAUCHI

 

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

 

Wata kotun bin hakkokin kungiyoyi da kamfanoni wacce ke da zama a Bauchi wato National Industrial court ta bukaci tsoffin kansilolin Jihar Yobe 171 dukkan su,  su bayyana a gabanta ranar Alhamis 24/11/2022 don bayar da shaida game da hakkokin su na kudin kammàla wa’adin aiki da suka Yi a shekarar 2013 zuwa 2015 Wanda  suke neman gwamnatin Jiha Yobe ta biya su.

 

 

Wakilin mu ya halarci zaman kotun da ya gudana a Bauchi, inda ya tattauna da jagoran kansilolin Honorabul Ali Gaje Gashua, inda ya ce suna cikin kansiloli 171 da suka yiwa gwamnati biyayya har suka kammàla lokacin su na wakilcin amma ba a biya su hakkin su na gama aiki ba Wanda kowane mutum zai samu daga naira milyan biyu zuwa hudu ya danganta da ofis da mutum ya rike.

 

Don haka yace ya zamo wajibi su yi Kara don a biya su hakkin su musamman ganin an biya mutane da dama da suka rike mukamai amma su an ki biyan su.

 

Don haka ya roki kotu ta bi musu hakkin su, amma wasu marasa kishi sai suka rubuta takardun janyewa  daga shari’ar da cewa wasu mambobin su ne suka rubuta alhali duk gasu sun bayyana a kotun da bakin su Kuma sun bayyana basu da masaniyar Wanda ya rubuta takardar da sunan su don a yi Karan tsaye wa shari’ar.

 

Saboda haka alkalin kotun Mai shari’a Mustapha Tijjani ya bukaci dukkan kansilolin su daure su shigo motoci zuwa Bauchi don kotu ta gan su a zahiri ta tabbatar da shaida kafin ta yanke hukunci.

Shima Alhaji Zubair Kansila Bursali cikin jawabinsa ga manema labarai ya bayyana cewa suna rokon gwamnatin Yobe ta biya su hakkokin su don su samu abin lura da kan su da iyalan su, musamman ganin sun Yi aiki na gaskiya tare da yiwa gwamnati biyayya ya kamata a tausaya musu a biya su hakkinsu.

 

Tsohon Kansila Garba Sarki Potiskum cikin jawabinsa ya bayyana cewa shi gurgu ne Kuma da haka yake gwagwarmayar neman hakkin su, don haka za su ci gaba da fafata shari’a har lokacin da za su ga hukuncin da kotu zata zartas, don haka ya ce sun gamsu da yadda kotun ke gudanar da shariar Kuma suna gani za a musu adalci wajen tilasta gwamnatin jihar ta Yobe don ta biya su hakkokin su.

 

Bayan muhawara tsakanin lauyoyin masu Kara Ahmed Igoche da lauyan gwamnati Don Aguse, alkalin kotun Mai shari’a Mustapha Tijjani ya bukaci dukkan kansilolin 171 su bayyana a gaban kotun ranar 24 ga watan Nuwamba na 2022 don bayar da shaida kafin a kai ga yin hukunci.

 

Kotun Kuma ta bayyana gamsuwarta da shaidun da aka kawo gabanta Wanda suka cika kotun makil, bayan haka Kuma suma kansilolin sun nuna gamsuwa da yadda shariar ke tafiya.

About andiya

Check Also

The Daily Hug For Appreciation 2023

The daily hug for 28/11/23 is this appreciation of an echo shared by my dear …

Leave a Reply

Your email address will not be published.