Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokokin Jiha da ke zamanta a Kano ta yi watsi da zaben Yusuf Umar Datti na NNPP bayan bai yi murabus daga Jami’ar Bayero Kano kwanaki 30 gabanin zaben ba.
Mai shari’a Ngozi Flora Azinge ta umarci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta ajiye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Datti a baya tare da bayyana Musa Ilyasu Kwankwaso a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u na biyu a zaben Kura/Madobi/Garun Malam a ranar Fabrairu 2023.