Home / Big News / EFCC Ta Damke Mutanen Chaina Biyu Da Zargin Cin Hancin

EFCC Ta Damke Mutanen Chaina Biyu Da Zargin Cin Hancin

Imrana  Abdullahi
Hukumar da ke fafutukar yaki da masu kokarin karya tattalin arzikin kasa da cin hanci da karbar rashawa da kuma al’amuran da suka shafi kudi shiyyar Sakkwato sun samu nasarar Damke wadansu yan kasar Chaina biyu da suka yi kokarin bayar da cin hanci miliyan Dari ga shugaban shiyya na hukumar.
Ofishin shiyyar Sakkwato na Efcc ya samu nasarar kama mutane biyu yan kasar Chaina  da suka hada da Mista  Meng Wei Kun da  Mista Xu Koi da laifin bayar da cin hanci kudi naira miliyan 50 ha shugaban Shiyyar Mista Abdullahi Lawal.
Hakika wannan ofishin na shiyyar Sakkwato ya kara fito da Daraja da Martabar yan Nijeriya a kasashen duniya baki daya.
Don haka ake kira ga Gwamnati karkashin Muhammadu Buhari ya yi wa wannan mutum shugaban shiyya gagarumar sakayya.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.