Home / Kasashen Waje / KOWA YAJE YA KARBI KATIN ZABENSA – DOKTA AMINATOU ABDOULKARIM

KOWA YAJE YA KARBI KATIN ZABENSA – DOKTA AMINATOU ABDOULKARIM

An yi kira ga daukacin al’ummar kasar Jamhuriyar Nijar mazaunan Najeriya da suje wuraren da suka yi rajista domin karbar katunan zabensu da za su yi zabe da shi a ranar zabe.

Hajiya Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa ta sakon murya da ta aikewa al’ummar Nijar mazauna Najeriya.

“Hakika jami’an hukumar zabe na SENI daga kasar Nijar sun iso Najeriya kuma tuni sun kai katunan zabe a wuraren da suka yi wa jama’a rajista domin kowa ya karbi katin zaben sa da zai yi amfani da shi a ranar zabe mai zuwa”.

” Ina yin kira ga daukacin jama’a musamman ma mata da su hanzarta zuwa wuraren da suka yi rajista su nuna takardar da aka ba su a lokacin da aka yi masu rajista domin karbar katin zaben su da za su yi amfani da shi a ranar zabe mai zuwa”.

A cikin sanarwar Dokta Aminatou Abdoulkarim ta yi wa kowa fatan alkairi baki daya.

About andiya

Check Also

Return Our Property, Documents In Your Possession, SWAN Tells Ex-President Sirawo

    The Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) has warned its erstwhile National President, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.