Bashir Bello daga majalisar Abuja
Sanata Nasiru Sani Zangon Daura, ya bayyana batun kudirin matsalar tsaron da ya gabatar a gaban majalisa da cewa batu ne na baki dayan yan majalisar da suka fito daga Jihar Katsina amma ba na shi kadai ba.
Sanata Nasiru Sani Zangon Daura ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja.
Sanata Zangon Daura ya ci gaba da bayanin cewa kasancewar batun harkar tsaro lamari ne da ya shafi dukkan kowa don haka ne ya gabatar da shi a gaban majalisa da yawun dukkan wani dan majalisar da ya fito daga Jihar Katsina, saboda haka kenan batun al’ummar Jihar ne baki daya ne domin su wakilan jama’a ne.
Sanata Zangon Daura ya kara da cew duk mai bibiyar irin abubuwan da ake yi a majalisun kasarbzai ga lallai akwai wani abu da ake yi mai kama da wannan kudirin da ya gabatar a gaban majalisar Dattawa a kan batun matsalar tsaron da ake fama da shi.
“Ko a Jihar mu ta Katsina kowa ya san Gwamna baya Bacci a kullum ya na ta daman aiki ba Dare ba rana domin ganin an samu magance wannan matsalar duk wanda zai yi magana tsakani da Allah zai fadi hakan”, inji Nasiru Sani Zangon Daura.
Ya ci gaba da cewa duk abin da ake yi ana yo ne domin aga an samar da zaman lafiya da tsaro acikin Jihar saboda haka idan an duba sosai za a ga cewa ba matsalar Jihar Katsina bace kawai ta arewacin kasar ne baki daya kuma idan an sake kasar baki daya dauka za ta yi kuma ko a yanzu ma yaya aka kare saboda duk wata shiyya a kasar nan da za ka taba lallai sai ka ga akwai wata matsalar ta tsaro .
“A yankin Katsina ta Arewa da nake wakilta lamarin da sauki kwarai da gaske, amma a yankin Katsina ta tsakiya da ta Kudu, Jihohin Zamfara, Sakkwato, Kebbi da Jihar Neja duk ana fama da wannan matsala ta tsaro saboda a da can ana maganar Arewa maso Gabas ne da ake fama da Boko Haram amma a yanzu lamarin ya dawo nan Arewa maso Yamma.
Gwamnonin nan na Arewa maso Yamma suna ta kashe makudan miliyoyin kudi domin ganin an yi maganin wannan matsalar, musamman wajen taimakawa jami’an tsaron su gudanar da aikinsu duk da irin wadannan makudan kudin da ake kashewa ta fuskar tsaro amma lamarin yaki ci yaki cinyewa domin har yanzu mutane ana cikin tashin hankali har ma ya koma kamar ruwan Dare kullum ni da abokan aiki na daga Jihar Katsina kamar Sanata Muktar Dandutse da Sanata Abdul’Aziz Yar’aduwa a koda yaushe za su rika bayanin cewa an shiga gari Kaza ko an kwashe mutane kaza da suke a wuri kaza an samu matsala a wuri kaza lamarin dai ba dadin ji ko kadan don haka dole ne mu tashi tsaye domin a magance matsalar.