Home / KUNGIYOYI / Kungiyar KADDA Ta Karrama Farfesa Shehu Sale

Kungiyar KADDA Ta Karrama Farfesa Shehu Sale

Daga Imrana Abdullahi

Sakamakon kokarin aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma a fannonin gudanar da rayuwa daban daban yasa hadaddiyar kungiyar ci gaban jama’ar Doka (KADDA) da ke cikin garin Kaduna ta Karrama babban Likitan kula da lafiyar kwakwalwa da karansa ya kai tsaiko,  Farfesa Shehu Sale da nufin kara karfafa masa Gwiwar ci gaban ayyukan da yake yi.

Kafin kungiyar ta bashi wannan lambar karramawa sai da ta fayyacewa jama’a dalilan da suka Sanya kungiyar ta bashi lambar samawa jama’a dimbi abin yi da taimakawa kasa baki daya musamman a fannin samar wa jama’a ingantacciyar lafiya.

Gagarumin taron Karrama Farfesa Shehu Sale da kuma wadansu fitattun mutane a ciki da wajen Najeriya ya gudana ne a cikin dajin taron makarantar Nurul qur’an da wasu ke wa lakabi da Nuriya a kan titin Katsina kusa da Unguwar Oriya kwata.

Jim kadan bayan kammala taron karramawar Farfesa Shehu Sale ya bayyana cikakkiyar gamsuwarsa da irin yadda kungiyar KADDA ta bashi wannan lambar karramawa wanda hakan ya sa ya kara zama Gwarzo da kuma kaimin ci gaba da tashi tsaye wajen yi wa kasa da al’ummarta hidima a dukkan fannonin inganta rayuwar bil’Adama baki daya.

“Hakika na ji dadin wannan karramawar da aka yi Mani domin ban taba tsammanin za a bani wannan Karramawa mai girma da daraja irin wannan ba da ta kara daga daraja da martabar da nake da ita, don haka ina yi wa Allah godiya da wannan baiwar da ya yi mani”.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.