Home / KUNGIYOYI / KUNGIYAR KWADAGO TA GARGADI GWAMNATIN JIHAR KADUNA KAN TSOMA BAKI A HARKOKIN TA

KUNGIYAR KWADAGO TA GARGADI GWAMNATIN JIHAR KADUNA KAN TSOMA BAKI A HARKOKIN TA

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna ta bayyana matukar rashin jin dadin ta a kan yadda Gwamnatin Jihar ke kokarin yin  katsalandan a cikin harkokinsu.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a lokacin da shugaban kungiyar na Jihar Kaduna kwamared Ayuba Magaji Suleiman ke yi wa manema labarai jawabi a dakin taron kungiyar da ke Kaduna.
Ayuba Magaji Suleiman ya kuma yi kira ga yayan kungiyar da kada su amince da yunkurin Gwamnatin Jihar Kaduna na kokarin tauye masu yankin da suke da shi a kundin tsarin mulkin Nijeriya da na aikin kwadago.
“Akwai wani hukuncin da mai shari’a O
A. Obaseki – Osaghae, cikin wata shari’a mai lamba NO. NICN/QBJ/77/2021, tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna da kungiyar malaman makaranta NUJ reshen Jihar Kaduna,da aka yanke hukunci a ranar 2 ga watan Disamba 2021, da kotun shari’ar harkokin kwadago ta Gwamnatin tarayya da ke Abuja inda kotun ta tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kadina ba ta da ikon tsoma baki a harkokin tafiyar da kungiyoyin kwadago a Jihar.
“Sakamakon wannan hukuncin muna son yin bayani karara cewa a matsayin mu na kungiyar kwadago mun yi watsi da irin yadda Gwamnatin Jiha ke yin shisshigi a harkokin kungiyar Kwadago, saboda haka muke yin kira ga dukkan yayan kungiyar da suka kasance ma’aikata sakamakon irin yadda kundin tsarin mulki da dokokin kasa suka yi bayani dalla dalla”, in ji Ayuba.
Ayuba Magaji, ya ci gaba da cewa irin abin da Gwamnatin ke aikatawa tsari ne da ke bayani a fili ana yin kazalanda ne a cikin harkokin tafiyar da kungiyar kwadago kamar yadda yake a harkokin kungiyar na kasa da kuma na tsarin kasa da kasa.Kungiyar ta kasa da kasa a wani babban taron an yi bayani sosai a game da batun yancin haduwa a karkashin wata kungiya a doka mai lamba NO.87 na shekarar 1946 da kuma wani taron da aka shirya mai lamba NO. 98 a shekarar 1949, a game da yancin haduwa a samar da wata yarjejeniyar kungiya, Najeriya ma ta samu shiga wannan tsarin tun a shekarar 1963, kuma ya na a cikin sashe na 17, 23,24 da kuma 25 na dokar kwadago a shekarar 2005.
Saboda haka muke shaidawa daukacin ma’aikata da su tabbatar sun yi aiki da abin da ke cikin kundin tsarin mulki da kuma dokar kasa ba tare da wani ko wasu sun rude su ba.
Ayuba ya ci gaba da bayanin cewa kada da jama’a su mance a shekarar 2016 ma Gwamnatin ta yi irin wannan bayar da takarda ga ma’aikata ana tambayarsu ko suna tare da kungiyar kwadago ko A’A wanda hakan ba dai – dai ba ne a tsarin kwadago da kuma dokar aiki.
Saboda haka wannan rabon takardar ya kasance na biyu kenan da ake yi tun hawan mulkin wannan Gwamnatin.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.