Home / KUNGIYOYI / Kungiyar Makiyaya Ta KACRAN Ta Yabawa Gwamna Buni kan Hak’uri Da Juriya Wajen Harkokin Jagorancin Jama’a

Kungiyar Makiyaya Ta KACRAN Ta Yabawa Gwamna Buni kan Hak’uri Da Juriya Wajen Harkokin Jagorancin Jama’a

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Kungiyar makiyaya ta Kulen Allah (KACRAN) ta yabawa gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe bisa ga yadda yake nuna hakuri da jajircewa ga jagorancin da ya kewa al’ummar Jihar ba tare da gajiya ba ko nuna halin ko oho.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar na kasa Khalil Muhammad Bello a ganawar sa da manema labarai, Jim kadan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na kungiyar da aka gudanar a babban dakin taro na Sakataren Gwamnatin Jihar da ke garin Dake garin Damaturu.
Shugaban ya kara da cewa, kungiyar su ta Kulen Allah ne ta ga ya dace ta kira taron manema labarai tare da shaida wa duniya alfanun da ta ke da ta samu a karkashin Gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni.
Honarabul Khalil Muhammad Bello ya ce a jihar Yobe ne kawai ake nada makiyayi da ke zaune a daji da shanunsa a matsayin mataimaki na musamman ga gwamna.
Ya lura cewa wannan karimcin ya cancanci yabo ya kara da cewa sauran alamu suna da yawa da za a ambata irin abin son barka da gwamna Buni Ya yi ga makiyaya.
Shugaban kungiyar ya yi amfani da Wannna dama wajen taya Gwamna Mai Mala Buni murnar kammala wa’adinsa na farko cikin nasara tare da samun nasarar sake lashe zaben gwamna da ya kai shi ga kaiwa ga karo na biyu cikin hukuncin Allah.
Don haka shugaban na KACRAN ya bada tabbaci ga gwamnan cewar, a kowane lokaci a shirye suke don ganin sun rufa masa baya don ganin ya cimma nasarar gudanar da wannan gwamnati cikin nasara da kwanciyar hankali don amfanuwa al’ummar Jihar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.