Home / KUNGIYOYI / KUNGIYAR MATASA KWARARRU ‘YAN KANO MAZAUNA KUDANCIN NAJERIYA SUN YABAWA SARKIN KANO AMINU ADO BAYERO KAN SHUGABANCI NAGARI

KUNGIYAR MATASA KWARARRU ‘YAN KANO MAZAUNA KUDANCIN NAJERIYA SUN YABAWA SARKIN KANO AMINU ADO BAYERO KAN SHUGABANCI NAGARI

Daga Imrana Abdullahi
A wani zama na musamman da kungiyar matasa kwararru ‘yan asalin jihar Kano, mai suna Kano Youth Professionals, mazauna kudancin Najeriya da kuma Arewa ta Tsakiya, su ka yi a Kaduna yau Talata, sun yaba matuka da yadda Sarkin Kano Aminu Ado Bayero yake tafiyar da mulkinsa.
Musamman wajen la’akari da yadda yake nuna tausayinsa ga al’ummar sa da jama’ar kasa gaba daya.
A wata takardar bayan taro da shugannin kungiyar na Kudu da na Arewa ta Tsakiya Mansur Sulaiman da Bashir Sa’ad su ka sa wa hannu, sun ce “Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero kullum ya na nuna halin dattako da tausayi wajen tafiyar da mulkinsa.”
“Mun ji dadi matuka da gaske yadda mu ka ga ya yi kira ga yan kasuwa da su sassauta farashin kayan abinci da kara kira ga masu hannu da shuni da su taimakawa talakawa ganin yadda wata mai alfarma na Ramadan ya kusanto,” in ji takardar bayan yaron.
Su ka ci gaba da cewa sun ji dadi ganin yadda Sarkin ya yi kira ga gwamnatin tarayya karkashin shugaba Bola Tinubu da ta kara duba wahalar da talakawa ke ciki na fatara da yunwa. Ya yi kiran ne lokacin da uwargidan shugaban kasar, Remi Tinubu ta kai wata ziyara fadar Sarkin kwanan nan.
Kuma sun yaba da wasu yan gyare gyare da su ka ce gwamnatin tarayyar ta fara. Su ka ce “Irin wadannan abubuwan alheri na Sarkin Kano su na sa wa mu na tunawa da marigayi Mai Martaba Ado Bayero.”
Ganin irin hobbasar da Sarkin ke yi wajen rokon shugannin kasa da a fito da wasu manufofi dan inganta rayuwar al’umma, ‘yan wannan kungiya sun roki gwamnatin tarayya da ta hada hannu da Sarakuna wajen kara wayar da kan al’umma kan tsare tsaren gyaran kasa da gwamnatin ke yi.
“Kuma ba mu kara sarawa Mai Martaba ba sai da mu ka kara ganewa cewar shi fa ba burinsa ne jawo hankalin mutane kan sa dan wata manufa ko bukata ta kashin kansa ba.
Shi Mai Martaba kullum zancen sa daya ne, wato ta yaya talaka zai samu sararawa a rayuwa. Kullum abinda ya sa a gaba shine ya ba shugabanni shawara bisa girmama juna saboda a saukaka rayuwa da halin kaka-ni-ka-yi da jama’a ke ciki,” in ji takardar.

About andiya

Check Also

Return Our Property, Documents In Your Possession, SWAN Tells Ex-President Sirawo

    The Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) has warned its erstwhile National President, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.