Home / KUNGIYOYI / Kungiyar NURTW Ta Taimakawa Direbobi 360 Masu Bukatar Tallafi Da Dubu Goma Da Turamen Zannuwa Ga Mata 30 A Kaduna

Kungiyar NURTW Ta Taimakawa Direbobi 360 Masu Bukatar Tallafi Da Dubu Goma Da Turamen Zannuwa Ga Mata 30 A Kaduna

Matan Direbobi da suka rasu 30 aka ba su dubu Goma da Turamen zannuwa

Mata 30 dubu Goma da Turamen Zannuwa

Maza dari 330 dubu Goma Goma kowannensu

Sakamakon irin farin ciki da jin dadin an san da su direbobi Maza da kuma Matan da mazajensu suka   mutu suka bari su kuma an ba su Turamen Zannuwa da naira dubu Talatin kowaccensu wanda sakamakon jin dadin da farin cikin da suka shiga wadansunsu nan take suka barke da kuka suna murna sakamakon tsananin jin dadin an tuna da su har aka taimaka masu da kudi.

Da yake tattaunawa da wakilinmu ya dandalin Sada zumunta na whattsapp Alhaji Aliyu Tanimu Zariya, shugaban kungiyar direbobi (NURTW) reshen jihar Kaduna kuma mataimakin shugaba na kasa, ya bayyana cewa babban dalilin da yasa suka yi tunanin bayar da tallafi ga direbobi masu bukatar tallafi da kuma matan direbobin da mazajensu suka rasu suka barsu shi ne sakamakon irin halin matsin tattalin arzikin da ake ciki ne da lura da halin da mutanen ke ciki yasa aka lalubo ainihin mutane dari uku da Sittin aka tallafa masu wanda hakan ma zai taimakawa Gwamnati baki daya.

Aliyu Tanimu Zariya ya ci gaba da bayanin cewa wadansu direbobin sun samu hadari ne wasu sun rasa idanu wadansu sun rasa kafa, wasu hannuwansu wasu ma sun dawo jikinsu baya ma aiki sakamakon samun hadari da dai sauran wadansu larurori na rayuwa daban daban duk da cewa mun yi kokarin zuwa ga Gwamnati ko Allah yasa a samu tallafin amma dai har yau bai samu ba.

“Hakan yasa a cikin dan abin da muke samu ta hanyar sayar da tikiti a tashoshin mu sai muka ga ya dace a rika tara wani abu domin a rika taimakawa irin wadannan mutane da muka taimakawa a yanzu, an ba mutane dari 360 tallafin a cikinsu akwai Mata. An ba Maza naira dubu Goma Goma har mutum dari 330 sai kuma mata su 30 da mazajensu suka rasu da aka ba su naira dubu Goma Goma da Turamen Atamfa kowannensu, kuma hakan kashi na farko ne da mun sake samun zarafi nan gaba za a sake yin wani kashi na biyu”, inji A Tanimu Zariya

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.