Related Articles
MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Wata qungiyar jin qai ta matasa mai suna Mercy Charity Givers dake garin Kafanchan a qaramar hukumar Jama’a ta jihar Kaduna ta kaiwa ‘yan gidan yarin Kafanchan ziyara tare da raba musu kayan abincin buda baki.
Da take jawabi ga ‘yan gidan gyara halinka, shugabar qungiyar, Aisha Ibrahim ta ce maqasudin kawo ziyara tare da bayar da tallafin kayan abincin garesu shi ne don nuna qauna da jin qai tare da qarfafa musu gwiwa kan haquri a irin halin da suka tsinci kansu.
Aisha, wacce ta jawo hankalin fursunonin da su ci gaba da addu’ar samun mafita daga inda suka tsinci kan su, ta kuma yi kira a garesu da su xauki darasi daga zamansu a gidan yarin don qoqarin gyara halayensu idan sun fito.
“Mun san wasunku qaddara ce ta hau kan su, wasu kuma qananan basussuka ne yayinda wasu kuma sun aikata laifuffuka ne suka tsinci kansu a nan, amma duk da haka muna fatan watarana ku fita daga gidan sannan ku zamo masu amfani a cikin al’umma.” Inji ta
Shi kuwa Muhammad Sani Adamu, wani mamba a qungiyar, qalubale ya jefawa fursunonin da kada gwiwarsu ta karaya don sun tsinci Kansu a wannan yanayin, maimakon haka su yi tunanin fitattun mutanen da suka tava tsintar kansu a gidan yari amma daga baya suka zama wasu a cikin al’umma.
“Don haka ina qalubalantar Ku da ku yi qoqari ku zamo kamar waxancan ba irin gurvatattun da suke daxa kangarewa suna tozarta quruciyarsu ba.” Inji shi
Yayin da yake jawabi a madadin ma’aikatan gidan gyara halinka na garin Kafanchan, Mataimakin Kwanturola Lamiya Israel, ya godewa matasan da su ka tuna da waxanda ke tsare a gidan yarin wanda an kwana biyu ba a kawo musu irin wannan tallafin daga waje ba.
Israel, ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga fursunonin da su yi wa kansu qiyamullaili duk wanda ya fita kada ya maimaita irin laifin da ya yi don kada a maido da shi gidan, a cewarsa, hakan ba dabara ba ce.