Home / KUNGIYOYI / Kungiyar Matasan Borno (BOYIC) Na Goyon Bayan Kashim  Shettima A Matsayin Mataimakin Tinubu

Kungiyar Matasan Borno (BOYIC) Na Goyon Bayan Kashim  Shettima A Matsayin Mataimakin Tinubu

Daga Sani Gazas Chinade, Maiduguri
Kungiyar matasan Borno (BOYIC) ta yi alkawarin nuna goyon bayan su dari bisa dari ga Kashim Shettima a matsayin mai rufa baya gaba dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Bola Ahmed Tinubu don kaiwa ga nasara a zaben kasa da ke tafe a shekara mai zuwa ta 2023.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya zabi Shettima ne a matsayin mataimakinsa, lamarin da ke barazana ga ruguza jam’iyyar, inda fitattun jiga-jigan jam’iyyar suka bar jam’iyyar tare da magoya bayansu.
 A cewar BOYIC, tikitin takarar shugaban kasa na musulmi da musulmi “nasara ce” ga Jam’iyyar ta APC ta yadda jam’iyyun siyasa masu adawa a kasar za su sha kaye cikin yardar Allah.
Da yake bayyana goyon bayansu, a wani taron manema labarai a Maiduguri, shugaban kungiyar, Muktar Gubio, ya bayyana cewa fitowar Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu, wata dabara ce ta lashe zabukan da ke tafe a Arewa.
Da yake taya Shettima murna, ya ce: “Muna so mu hada kai da miliyoyin ‘yan Najeriya wajen taya Senata Kashim Shettima murnar zabensa na zama mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.”
Ya bayyana nadin tsohon Gwamna Sanata mai ci a matsayin zabi mafi kyau da jam’iyyar ta yi tun 2014.
Shi tsohon Gwamna kuma Sanata mai ci a yanzu Kashim Shettima ya nuna kwazo da himma wajen kawo sauyi a kasar da yanayin rayuwar jama’a, in ji shi.
Gubio ya bayyana kwarin gwiwar cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa zai yi amfani da kwarewarsa a matakin kasa idan aka zabe shi a 2023.
Don haka ya  godewa Bola Ahmed Tinubu kan zaben Shettima ya zama mataimakinsa wadda yin hakan zai taimaka masa matukar gaske wajen kaiwa ga cimma burin sa na zama shugaban kasa cikin hukuncin Allah SWT.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.