Home / KUNGIYOYI / Kungiyar Matasan Kitistoci Ta Arewa Sun Yabawa Gwamnatin Tarayya A Game Da Bayar Da Tallafi A Kan Kudin Sufuri 

Kungiyar Matasan Kitistoci Ta Arewa Sun Yabawa Gwamnatin Tarayya A Game Da Bayar Da Tallafi A Kan Kudin Sufuri 

Kungiyar matasan Kiristoci (NCYP) da ke yankin arewacin Najeriya sun bayyana cikakken farin ciki da gamsuwarsu game da abin da Gwamnatin tarayya ta yi na bayar da tallafin sufuri da kashi Hamsin (50) cikin dari a lokacin bukukuwan Kirsimati da na sabuwar Shekara da tallafin zai shafi wadansu muhimman hanyoyi guda 22 a duk fadin kasar.
Kamar yadda kungiyar ta bayyana cewa Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta nuna a fili cewa ta na aiwatar da dukkan ayyukanta ne domin ci gaban talakawan kasa, wanda hakan yasa kungiyar matasan Kiristoci kwararrun a fannonin ilimi daban daban mai suna NCYP suka bayyana godiyarsu da jin dadin abin da Gwamnatin Gwamnatin aiwatar ta hanyar Sanya rayuwar talakawan kasa a cikin walwala da yanayi mai kyau.
Kuma daukar wannan mataki ya tabbatar da cewa kokarin da Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi na cire tallafin man fetur ashe kungiyar matasan Kiristoci na duba komai sannu a kan hankali ta yadda yan kasa za su amfana.
A matsayin mu na kungiyar Kiristoci, ta NCYP suna taya daukacin Kiristoci murnar samun hakan a duk fadin kasa baki daya. Saboda wannan cire tallafin zai taimakawa Kiristoci su samu sukunin yin tafiye tafiye domin aiwatar da bukukuwan kirsimati da na sabuwar shekara tare da iyalai, yan uwa da abokan arziki a duk fadin kasa baki daya. Kuma hakan zai kara nuna Soyayya, yan uwantaka da bayyana al’adun jama’a a lokacin bikin kirsimatin.
Kungiyar NCYP na yin kira ga Kiristoci Kiristoci sauran jama’a da su yi amfani da wannan dama domin cin moriyar shirin taimakawa rayuwar jama’a da Gwamnatin tarayya ta fito da shi, wanda aka ware zai fara aiki tun daga ranar 21 ga watan Disamba, 2023, zuwa ranar 4 ga watan Janairu, 2024.
Muna yin kira ga kowa da kowa da ayi tafiya cikin hankali kwanciyar hankali da lumana domin a samu damar yin Hutu tare da yan uwa, masoya da abokan arziki a lokacin wannan hutun kirsimati da sabuwar shekara lafiya.
Kungiyar ta ci gaba da bayanin cewa suna yin kira ga hukumomin jami’an tsaro baki daya da su tabbatar da cewa an yi hutun kirsimati da na sabuwar shekara lafiya a duk fadin kasa baki daya.
Muna yin kira ga Kiristoci da su ci gaba da yin addu’a domin samun nasarar mulkin shugaba Bola Tinubu musamman ganin irin yadda yake daukar matakin samun ci gaban kasa a kowa ne fanni, kuma musamman a bangaren samun ingantaccen tattalin arzikin kasa.
Bugu da kari kuma, kungiyar NCYP na kara bayar da kwarin Gwiwa ga dukkan masu harkokin sufuri da aka zaba da za a yi wannan aikin bayar da tallafin sufuri da su da suka hada da kamfanonin God is Good, Chisco Transport, Young shall Grow, God Bless Ezenata, Area Motors, da kuma hukumar kula da zirga zirgar sufurin origin kasa ta Najeriya ( NRC) muna yin kira a gare su cewa su tabbatar da cewa matafiyan da suka dace ne kawai na gaskiya suka samu cin mariyar shirin.
Kungiyar NCYP na nan za ta Sanya idanu a game da aiwatar da wannan aikin domin samun nasara a kasa baki daya.
A lokacin da muke samun gabatowar lokutan bukukuwan kirsimati da na sabuwar shekara, hakika ya dace mu yi bikin cikin murna da farin ciki, hadin kai da kuma godiya ga Allah.A saboda haka ne muke yin addu’ar samun yin Hutu cikin koshin lafiya da karuwar arziki ga dukkan yan Najeriya baki daya.
Sa hannu,
Isaac Abrak
Shugaban kungiyar matasan Kiristoci kwararru a fagen ilimi na arewacin Najeriya (NCYP)

About andiya

Check Also

KASUPDA Organizes Stakeholders Engagement Programme

Community in the approved regularization layouts areas in Kaduna Metropolis have been advised to co- …

Leave a Reply

Your email address will not be published.