Related Articles
MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Kungiyar Noman zamani ta kasa ta bayar da tabbacin cewa za su samar da ingantaccen tsarin da zai bayar da damar samar da Kaji a kowace Shekara guda miliyan 125 a duk fadin Najeriya da Jihar Bauchi da ke arewacin tarayyar Najeriya.
Da yake gabatar da jawabinsa wajen kaddamar da mata 65 masu kiwon Kaji a kowace karamar hukuma cikin Jihar Bauchi a ranar Alhamis da ta gabata, shugaban kungiyar masu Noman zamani ta kasa Dokta Aliyu Muhammad Waziri ya ce ana saran manoman Kaji su samar da miliyan 125 a kowace shekara.
Shugaban kungiyar na kasa Dokta Aliyu Waziri ya kuma shaidawa manoman Jihar Bauchi lokacin da yake tattaunawa da su cewa shi yasa suka zo Jihar Bauchi domin tabbatarwa da wadanda suka amfana da tsarin irin muhimmancin da wannan shirin yake da shi wanda dalilin hakan yasa suka bude ofishin a Jihar.
Dokta Aliyu Waziri ya ci gaba da cewa an shirya wannan kokarin bayar da tallafi ga manoma ne domin kowa ya samu gajiyar da ke tattare da shirin ta fuskar kiwon Kaji wanda hakan zai bayar da damar samawa jama’a wadataccen abinci da bunkasar tattalin arziki ga kasa baki daya.
Ya kuma yi wa mahalarta taron tattaunawar cewa Kungiyar Noman zamani na da muhimman shirye shirye guda biyar (5) da aka shirya su a tsanake domin samawa jama’a aikin yi ta fuskar Noma duk da nufin kawar da radadin talauci ha yan kasa kuma hakan ya taimaka wajen rage yawan kwararar jama’a daga karkara zuwa birane wanda hakan zai taimaki tattalin arzikin kasa a cimma nasarar da kowa ke bukata a Najeriya.
“Kungiyar NAMCS a shirye take domin taimakawa mambobinta a dukkan Jihohin da ke fadin tarayyar Najeriya da na’urorin Noma na zamani”, Inji Dan marayan Zaki.
“Tsarin da muka shirya domin ganin an yi Noma a Najeriya wani shiri ne da zai kara kawo gyara ta fuskar Noman zamani ta hanyar yin amfani da kayan aikin Noma na zamani domin ya kara taimakawa Noman ya zama abin sha’awa ga kowa, wanda hakan zai sa matasa su shiga cikin harkar gadan gadan”.
A jawabansu daban daban, Kwamishiniyar da ke kula da kungiyoyin gama kai kuma kwamishinan Noma, Sa’adatu Bello Kirfi, Jidauna Mbami bayar da tabbaci suka yi cewa Gwamnatin Jiha za ta bayar da dukkan taimakon da ya dace domin samun nasarar shirin.
A jawabin ta, shugabar shirin a Jihar Baichi, Fatima Gidado cewa ta yi mata masu kiwon Kaji domin kara bunkasa tattalin arzikinsu a Jihar za su kama batun Kiwon kaji gadan gadan da nufin rage radadin talauci, musamman a yankunan karkara.
Fatima Gidado ta ci gaba da bayanin cewa shirin zai taimaka kwarai wajen samun ci gaba sosai ta fuskar samar da aikin yi, rade radadin talauci da ingantar tattalin arzikin al’ummar Jihar baki daya.