Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Kungiyar wakilan kafofin yada labarai (Correspondents Chapel) dake karkashin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Yobe ta sanar da dakatar da Kauracewa yada labaran ayyukan gwamnati a jihar da a kwanakin baya ta yi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da shugaban kungiyar Ahmed I Abba da Sakatare Michael Oshoma suka sanya wa hannu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bayan sanarwar kauracewa ayyukan gwamnati da ta yi a jihar, shugabannin kungiyar masu aiko da rahotanni sun gana da shugaban ma’aikatan gwamna Mai Mala Buni, Alhaji Abdullahi Yusuf Gashua, inda aka yanke shawarar duba koken don magance matsalolin.”
“Saboda haka, kungiyar wakilan kafofin yada labaran jihar Yobe, Chapel, a taronta na gaggawa ta amince da dakatar da Kauracewar ayyukan gwamnati, saboda jajircewar da jami’an gwamnatin jihar suka nuna, duk da haka, za ta ci gaba da sa ido kan abubuwan da ke faruwa yayin da suke zaman jiran irin matakan da gwamnatin zata dauka kan koken na su ”
“Don haka kungiyar wakilan kafofin yada labaran na son sanar da jama’a cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kungiyar ‘yan jaridu ya dora mata.”