Kungiyar Yan Jarida Reshen New Nigeria Sun Karrama Forofesa Tabari
Mustapha Imrana Abdullahi
Kungiyar yan jarida reshen kamfanin jaridun New Nigeria da Gaskiya Ta Fi Kwabo sun karrama babban Daraktan asibitin Barau Dikko da ke Kaduna.
Kungiyar yan jaridar reshen kamfanin New Nigeria sun bayyana cewa sun ba babban Daraktan asibitin Barau Dikko wannan karramawa ne sakamakon irin aiki tukuru da Furofesa Muss Abdulkadir Tabari yake yi a babban asibitin na koyarwa mai suna Barau Dikko, da ya dade yana duba lafiyar jama’a a ciki da wajen Jihar Kaduna baki daya.
Kamar yadda yayan kungiyar suka bayyana cewa ” Mun lura sosai irin yadda asibitin karkashin shugabanci Furofesa Musa Abdulkadir Tabari suke duba jama’a dare da rana musamman a lokacin da ake wahalar yaki da cutar Korona, saboda haka ne muka dauki wannan mataki domin duniya ta Sani kuma ayi ko yi da abin da shugaban asibitin ke aiwatarwa ta yadda rayuwar jama’a za ta inganta”.
Kungiyar sun ci gaba da bayanin cewa a lokacin yaki da annobar Korona mun duba sosai inda a kullum muka rika bayar da rahoton yadda lamura ke gudana a wannan lokacin, saboda kamar yadda kowa ya Sani wadansu muhimman wurare da suka hada da kasuwanni, masana’antu, ma’aikatu da hukumomin Gwamnati duk a rufe suke amma shi wannan asibitin dare da rana suna aiki ba gajiyawa duk saboda a taimaki al’umma wajen samun lafiya”.
Da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da wannan Furofesa Musa Abdulkadir Tabari cewa ya yi hakika wannan karramawa ya ji dadinta kwarai saboda kamar yadda jama’a suka Sani suna yin aikinsu ne tare da Gaskiya a koda yaushe ashe jama’a da dama suna kallon abin da suke aiwatarwa har aka kawo ga karramawar nan hakika mun ji dadi da farin ciki kwarai.
Ya ce hobbasar da suka yi na aiki tare da dukkan ma’aikatan asibitin wani lamari ne na farin ciki tun da har akwai masu ganin abin da ake yi a wannan asibitin.
“Mun rika duba marasa lafiya baki daya ba sai lallai wadanda suka kamu da cutar Korona ba saboda a lokacin da ake kulle sakamakon annobar Korona mun kasance mu kadai ne, wanda ya kasance cewa wani aiki ne da ma’aikatanmu suke aiwatarwa a kowane lokaci domin kasa ta ci gaba.