Home / KUNGIYOYI / KUNGIYAR ZABARKANO SUN KADDAMAR DA SABABBIN SHUGABANNI 193

KUNGIYAR ZABARKANO SUN KADDAMAR DA SABABBIN SHUGABANNI 193

KUNGIYAR ZABARKANO SUN KADDAMAR DA SABABBIN SHUGABANN

…Muna Son A Kafa Hukumar Kare Muradun Kananan Kabilu A Najeriya
DAGA IMRANA ABDULLAHI
A kokarin kungiyar al’ummar Zabarmawa da suke yan asalin Najeriya na ganin sun kare muradu tare da tabbatar da inganta rayuwar jama’a yasa suka kira wani babban taro na kasa a garin Abuja domin kaddamar da sababbin shugabannin da za su jagoranci kungiyar.
Alhaji Isa Sahabi Bankanu, ya bayyana wa duniya cewa manufar wannan kungiyar ta al’ummar Zabarmawa an kafa ta ne domin ci gaba da taimakawa muradun yayanta da suka hada da Maza da Mata yara da manya kasancewar jama’ar Zabarmawa na a ko’ina a cikin fadin tarayyar Najeriya.
Ya dai bayyana hakan ne a wajen babban taron kaddamar da shugabannin kungiyar Zabrkano na kasa da Jihohi su 193 da aka yi a garin Abuja.
Alhaji Isa Bankanu, ya kara da cewa a matsayinsa na shugaban kungiyar na kasa ya na yin kira ga daukacin Zabarmawa a duk inda suka samu kansu su zama jakadu nagari a dukkan mu’amalar da za su yi tare da jama’a.
Bayan kaddamar da sababbin shugabannin da kuma karramawa wadansu mutanen da suka bayar da gudunmawa wajen ciyar da Zabarkano gaba a matakai daban daban a lokacin rayuwarsu, wasu kuma an karramasu da ransu, wadanda suka yi wafati yayansu ko makusantansu ne suka karbi lambar karramawar a madadinsu.
Dokta Lawwali Sani Kasgada, sakatare Janar ne na kungiyar Zabarkano ya bayyana cewa suna yin kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya mika wa majalisar kasa kudirin samar da hukumar kula da kananan kabilu na kasa mai suna “national Minority tribes development commission” (NMTDC) domin kara inganta al’amuran kasa baki daya.
Dokta Lawwali Sani Kasgada ya kuma bayyana a cikin takardar da ya karantawa manema labarai bayan kammala taron cewa suna jinjinawa tare da bayar da girmamawa ga Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Dokta Sa’ad Abubakar na uku, bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban kasa ba tare da gajiyawa ba.
Hakazalika a wajen manema labaran sun kawo hankalin yayan kungiyar da su kara tashi tsaye wajen neman ilimi da kuma shiga Adama masu a harkokin al’umma domin hakan zai ba su damar kwatowa Zabarmawa yancinsu a Najeriya baki daya.
Sun kuma bayar da wasu misalai inda ake samun wadansu matsaloli wajen fayyace yayan Zabarmawan Najeriya da kuma na kasar Nijar musamman ta fannin jami’an hukumar shiga da ficen al’umma ta kasa.
An kuma gabatar da jawabai cikin harshen Zabarmanci da Hausa har ma da Larabci a wajen taron na kungiyar Zabarkano.
Lauya Aliyu Ishaq Lolo ne ya Rantsar da shugabannin baki daya
Akwai dai tattaunawa da kuma irin yadda taron ya kasance da za mu kawo maku a sashin Turanci da Hausa.

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.