Home / News / LOKACIN BATA LOKACI, LADAN GANIN IDANU DA MUNAFUNCI YA WUCE – DIKKO RADDA

LOKACIN BATA LOKACI, LADAN GANIN IDANU DA MUNAFUNCI YA WUCE – DIKKO RADDA

Daga Imrana Abdullahi

Zababben Gwamnan Jihar Katsina Dokta Dikko Umar Radda ya bayyana wa jama’ar Jihar da duniya baki daya cewa lokacin yin duk wani aiki ko wasu al’amura domin ganin idanu ya wuce.

“Yin aiki domin munafunci, domin ganin idanu ko bata lokaci ya wuce a Jihar katsina”

Duk abin da muke bukata shi ne a bari mu sauke dimbin kalubalen da ke kan mu, sabida akwai manya manyan kalubale da dama a kawunan mu duk sakamakon irin yadda jama’a suka zabe mu da nufin suna jiran mu cika masu alkawari.

Dokta Dikko Umar Radda zababben Gwamnan Jihar Katsina ya bayyana hakan ne a wajen wani gagarumin taron da aka yi inda ya fayyace komai danga ne da dimbin bukatar da ke akwai na jiran da jama’a ke yi masu ayi masu ayyukan da aka yi masu alkawarin za a yi masu  a lokacin da ake gudanar da Yakin neman zabe

“Daman wadansu sun ce wannan yaron wahalarshi za a sha, to my babban abin da ke gaban mu shi ne cika aiki kamar yadda ya dace ta yadda za a samu ci gaban rayuwa ba dadi ba kari a kan hakan, saboda haka ne nake tabbatar maku da cewa lokacin yin wadansu abubuwan irin can dauri duk sun wuce misali yin abu domin ganin idanu da dai makantan su .

A lokacin da wakilin mu ya zagaya da kuma tuntubar wadansu mutane ta wayar Salula domin jin ta bakinsa a game da yadda suke gani da kuma tsammanin Gwamnatin Dikko Radda ta kasance kasancewarsu yan asalin Jihar katsina da suka Jefa kuri’arsu sai suka ce da farko dai muna son kada a mance da irin alkairan da aka yi mana.

Musamman a fannin tsaron lafiya da dukiyar jama’a sai kuma a fannin samun jin dadin rayuwar mu a bangarori daban daban da suka hada da lafiya, ilimi samar mana da tituna a birane da kauyuka da za su taimaka mana mu samu saukin gudanar da harkokin sufuri.

Ga dai wadansu abubuwa nan da dama na ci gaba da muke gani a cikin duniya

Sai kuma wasu da suka ja hankalin Dikko Umar Radda da cewa ya tabbatar ya yi hankali da yan bani na iya da wadanda ke son biyan bukatun kansu a kan komai na rayuwar duniya.

Wasu kuma sun ce suna jiran ganin yadda za a inganta harkokin Noman Rani da na Damina da kuma koyawa jama’a sana’o’in hannu wanda duk da sune ake samun ci gaba a duniya, domin wasu kasashe duk sun jaraba an kuma dace don haka muna son ganinsu a Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwanna Dokta Dikko Umar Radda.

Babban abin jira a gani dai shi ne ko yaya lamarin zai kasance lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan kowa ya gani ya ji da tabbatarwa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.