…Gwamnatin Dikko Radda Ba Ta Da Niyyar Sayar Da Kayan Abinci Ga Kowa
Daga Imrana Abdullahi
Kwamishinan ayyuka na musamman Alh Isah Mohammed Musa kankara ya bayyana jin dadinsa a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa.
Alh Isah Mohammed Musa ya yi matukar farin ciki da abin da ya gani a shiyyar Daura a lokacin da ya sanya ido a kan rabon kayan agajin a shiyyar.
Kwamishinan ya ce kayayyakin abinci na shinkafa da masara da aka raba a shiyyar suna da inganci kamar yadda gwamnatin jihar ta amince da su.
Ya ce tallafin an yi shi ne domin rage radadin da jama’a ke ciki, ya kuma yi kira ga jama’ar jihar da su jajirce wajen ganin gwamnati ta yi kokarin dakile kuncin tattalin arziki na cire tallafin man fetur.
Alh. Isah Mohammed Musa ya ce Gwamna Malam Umar Radda da ke jagorantar gwamnati ba ta da niyyar sayar da kayan abinci ga mutane duk da cewa wasu mutane na kiran hakan.
Kwamishinan ya ce idan aka yi la’akari da halin kuncin da ake ciki a halin yanzu bai dace gwamnati ta sayar da kayan agajin ba, ya kuma yi kira ga jama’a,wadanda suka amfana da su yi amfani da hatsin da aka ba su.
Alh Isah Mohammed musa ya nuna cewa a shirye ma’aikatarsa ta ke wajen gudanar da sahihin sa ido tare da sanya ido kan rabon kayayyakin, sannan ya yi kira ga kananan hukumomi da su ba ma’aikatar hadin kai domin cimma buri da manufofin gwamnatin jiha.
Kwamishinan ya yi kira ga dillalan hatsi da kuma da su ji tsoron Allah su guji karawa kayan abinci farashi ba bisa ka’ida ba domin amfanin Talakawa.
Hakazalika ya yi kira ga masu hannu da shuni da su tallafa wa mabukata, ya kuma yi kira ga wadanda suke da hatsi a shagunansu da su sayar wa jama’a a kan farashi mai rangwame