Daga Imrana Abdullahi
Domin samun ci gaba mai ma’ana a Najeriya, dole ne shugabanni su daidaita kalmomi da aiki tare da aiwatar da hanyoyin magance matsalolin da ake fuskanta a fage daban-daban na rayuwar jama’a.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ne ya ba da wannan shawarar, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wani taron tattaunawa na yini daya da shugabannin gargajiya na al’ummar da ba su isa ba a gidan Arewa, Kaduna a ranar Laraba 16 ga watan Agusta, 2023.
“A matsayinmu na shugabanni, ba mu rasa hanyoyin magance matsalolinmu ba, abin da muka rasa shi ne aiwatarwa.
“Muna magana da kyawawan yaruka kuma muna komawa gida ba tare da aiwatarwa ba.
“Mun sake dawowa muna magana iri daya ba tare da aiwatar da shawarwari ba.
“Ya kamata mu aiwatar da kudurorinmu don samun ci gaba,” in ji shi.
Sarkin Musulmi ya godewa Hakimai a fadin jihohin Arewa 19 da suka jajirce wajen ganin an samu nasarar aklurar rigakafin.
“Lafiya ita ce arziki, lafiyayyar kasa ce mai ci gaba Ya zama wajibi a matsayinmu na shugabanni mu tabbatar da an yi wa ‘ya’yanmu rigakafin cututtuka kamar cutar shan inna da sauransu,” ya jaddada.
Ya kuma godewa hukumar UNICEF da sauran masu hannu da shuni kan gudunmawar da suke bayarwa kan harkokin kiwon lafiya a kasar nan.
“Mun zo nan don tattaunawa mai mahimmanci don haka don Allah a ba da gudummawa.
Wanda ya sanya takalmi ya san inda ya tsinke,” ya shawarci shugabannin gargajiya
Ya bukace su da ka da su jajirce kan inda kalubalen da ke shafar rigakafin ke tattare da al’ummarsu.
Hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa NPHCDA tare da hadin gwiwar gidauniyar Sultan Foundation ne suka shirya taron.