Muhammad Bello mashawarci ga gwamna a kan harkokin yada labarai ya fitar da sanarwar rasuwar wadda aka rabawa manema labarai a jihar Sakkwato ya ce Allah shi ne mallakin komai da haka yake sanar da rasuwar mahaifinsa Shaikh Haruna Waziri Usman.
Ya ce Margayin ya rasu ne a gidansa da ke garin Tambuwal a ranar Alhamis yana da shekarru 96, a duniya.
Shehi shi ne jagoran darikar Tijjaniya a garin Tambuwal gaba daya, ya yi wa addinin Allah hidima sosai al’ummar garin Tambuwal da jihar Sakkwato musamman mabiya darikar Tijjaniya sun yi rashin gwarzo mai son taimakawa addinin musulunci.
THESHIELD Garkuwa