Home / Big News / Kungiyar Kwadagon Jihar Kaduna Ta Tallafawa Marasa Karfi

Kungiyar Kwadagon Jihar Kaduna Ta Tallafawa Marasa Karfi

Imrana Abdullahi
Kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna karkashin jagorancin kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ta Tallafawa mabukata da ke cikin al’umma da kayan abinci domin rage radadin zaman gida da ake ciki a kokarin hana yaduwar cutar Covid – 19 da ake kira Korona da take addabar duniya.
Ga daya daga cikin jerin matan da suka amfana da wannan Tallafi
Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ya bayyana wa manema labarai a harabar ofishin da ke Kaduna cewa sun duba irin halin da wadansu mutane daga cikinsu ke ciki da suka rasa aikinsu tun a shekarar 2016 sai kuma musakai da dai sauran marasa galihu a cikin al’umma.
Kwamared Ayuba ya ci gaba da bayanin cewa daga cikin irin dan abin da kungiyar keda shi ne suke kokarin taimakawa wadansu domin Sanya farin ciki a Fuskokinsu.
Ga wadda ta amfana nan itama daga wannan Tallafi
Daga cikin abin da aka rana sun hada da Shinkafa mai nauyin kilogiram 10, Gero mai nauyin kilogiram 10 sai Man girki da abin wanke hannu da ake kira sanitizer.
An dai kira jama’a ne da suka hada da kabilu daban daban daga cikin musulmi da Kirista tare da kungiyar musakai da aka ba su gurbin mutane 20.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.