Home / Labarai / Makarfi, Gummi da daruruwan jama’a sun halarci jana’izar Aliyu Abubakar Sokoto a Kaduna

Makarfi, Gummi da daruruwan jama’a sun halarci jana’izar Aliyu Abubakar Sokoto a Kaduna

Mustapha Imrana Andullahi

 

 

Manyan mutane ciki har da tsohon gwamnan jahar Kaduna Sanata Ahmed Mohd Makarfi, Birgediya Janar Abdul’azeez Abubakar Gummi da sauransu suka halarci jana’izar Marigayi Aliyu Abubakar Sokoto wanda aka fi sani da Aliyu Sokoto, tsohon manajan kasuwanci na Yar Yaya Motors, wanda aka gudanar karkashin jagoranci Shiekh Dr Ahmed Gummi a gidan Marigayi Shiekh Abubakar Mahmud Gummi dake Kaduna.


Marigayi Aliyu Sokoto ya rasu a jiya Larba a asibiti koyon aikin Likita na Barau Dikko a Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya.

Aliyu Abubakar Dingyadi fitaccen dan kasuwa a Kaduna ya kwanta dama bayan gajeruwar rashin lafiya

Dan uwan marigayin Yusuf Abubakar Dingyadi babban mai baiwa Gwamnan jihar Sokoto shawara akan Hulda da kafafen yada labarai, ya bayyana rasuwar dan uwan nasa a matsayin abin da ya girgiza dukkan dangi da iyalansu.

Dingyadi ya bayyana cewar mamacin mutumin kirki ne dake son taimakon jama’a.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.