Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Jihar Kano na cewa manajan kungiyar kwallon kafa na Kano Pillars Kabiru Baleria ya rasu yana da shekaru 57 a duniya.
Mai magana da yawun da yawun kungiyar, Rilwanu Malikawa Garu ne ya tabbatar da hakan.
Ya dai rasu ne a kano a wani asibiti mai suna (Doctors Clinic) bayan fama da wani rashin lafiyar da ba a bayyana ba.
Kuma tuni aka yi Jana’izarsa kamar yadda addinin Islama ya tanadar.