Home / Labarai / Manoman Sakkwato Suna Bukatar Takin Zamani Ba Soki burutsu  Ba – Inji PDP

Manoman Sakkwato Suna Bukatar Takin Zamani Ba Soki burutsu  Ba – Inji PDP

Daga Imrana Abdullahi

An jawo hankalin gwamnatin Jihar Sakkwato kan gaggawa da bukatar samar da takin zamani ga manoman jihar.

Wannan dai kokarin jan hankali daga Jam’iyyar PDP na zuwa a dai dai lokacin da ake ganin Gwamnatin Jihar karkashin APC ta karkata wajen al’amuran da suka saba da muradun jama’a kasancewarsu manoma ga kuma Damunar ba na ta yi zurfi.

Wannan kiran na zuwa ne duba da yadda har yanzu ba a samar da taki ba duk da cewa noman na bana ya kusa kai kololuwar sa.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Hassan Sahabi Sanyinnawal, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP reshen Jihar Sakkwato kuma aka rabawa manema labarai ta bayyana cewa.

Jam’iyyar PDP reshen jihar Sakkwato ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta yi biyayya ga wannan kira tare da gaggauta samarwa da kuma rarraba kayan Noma ga manoman jihar.

Hakan ne zai ba su damar zage damtse ayyukan noma da nufin samun abin da ya dace na samar da abinci a jihar da ma kasa baki daya.

Sanarwar, ta kuma bukaci jam’iyyar APC mai ci a jihar da ta ci bashin ganye daga gwamnatin da ta gabata wajen tabbatar da raba takin zamani da sauran kayan amfanin gona ga manoma a kan kari domin shi ne abin da al’ummar Sakkwato ke bukatar ganin abinci a kan teburinsu ba wai wasu matsalolin da ba dole ba.  .

A cewar sanarwar, jam’iyyar PDP ta shawarci gwamnati da ta mai da hankali kan abubuwan da ke da muhimmanci da kuma gaggawa ga al’ummar jihar, maimakon daukar matakan da ba su dace ba ta hanyar rayuwa da abin da zai ciyar da jihar gaba.

Jam’iyyar ta ce ta nuna matukar damuwa da yadda gwamnati mai ci ke mai da hankali kan abubuwan da ba su dace ba, maimakon batutuwan da ke da muhimmanci wajen inganta rayuwar al’ummar jihar baki daya.

PDP ta yi bakin ciki ta tuna cewa a wannan lokaci gwamnatin da ta shude a karkashin PDP ta samar da kuma rarraba takin zamani ga manoma a fadin jihar da kyakkyawar niyya ta samun girbi mai yawa.

Sanarwar ta bukaci manoman da su hakura da lamarin domin kuwa gwamnatin APC a jihar ta fi mayar da hankali kan abubuwan da ba su da amfani fiye da abin da zai kyautata wa jihar da al’ummarta.

Don haka jam’iyyar PDP ta bukaci gwamnatin jihar da ta mai da hankalinta wajen kyautata rayuwa ga al’ummar jihar, maimakon munanan al’amura da ke biyan bukatun son zuciya kawai.

Sanyinnawal ya kara da cewa ” a cikin lokaci ne ya dace ayi komai, kuma lokacin da za a yi gaggawar daukar mataki shi ne yanzu,” in ji Sanyinnawal.

About andiya

Check Also

Northern govs meet in Kaduna, design regional economy, human capacity devt

    The chairman, Northern States Governors’ Forum (NSGF), Muhammadu Inuwa Yahaya, has called for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.