Home / Labarai / Masarautar Jama’a ta soke bukukuwan Sallah

Masarautar Jama’a ta soke bukukuwan Sallah

 

 

Mai Martaba Sarkin Jama’a dake kudancin jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya bi sauran manyan masarautu dake jihohin da aka bayyana tsoron alamun bayyanar cutar korona wajen dakatar da bukukuwan Sallar layya.

 

 

Sarkin, yayi wannan kira ne a yau cikin takardar manema labarai da aka rabawa ‘yan jarida a garin Kafanchan, inda yace daukar matakin ya zama wajibi don taimakawa wajen daqile bulla ko yaduwar cutar Covid – 19 a jihar Kaduna da Najeriya baki daya.

 

 

A cikin sanarwar, Mai Martaba Sarkin Jama’a ya bukaci jama’arsa da su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga hukumomi kamar yadda aka sansu da yi, inda yayi fatan samun mafita daga cutar ta korona.

 

 

Baya ga yiwa al’ummar musulmi na duniya fatan yin sallah lafiya, Sarkin ya yabawa gwamnan jihar Kaduna da jami’an tsaro musamman na ‘Operation Safe Haven’ da na ‘yan sandan mobayil na yankin dake aiki ba dare ba rana wajen kwantar da duk wata barazana da wasu marasa son zaman lafiya ke son tayarwa a yankin masarautar da kewayenta, inda yayi kira ga kowane bangare da su rika kai kukansu ga hukuma a duk lokacin da suke ganin wani abu ba daidai ba maimakon kokarin daukar doka a hannu.

 

 

A kan gudanar da bukukuwan sallah ne a masarautar Jama’a dake cikin garin Kafanchan ta hanyar zagaya manyan titunan garin jim kadan bayan idar da sallar idi, sannan washegari a gudanar da hawan daushe inda Sarkin kan kewaya babban titin garin zuwa babban asibitin garin inda ya kan ziyarci marasa lafiya tare da yi musu addu’a sa bayar da gudummawa, sannan ya gana da shugabannin asibitin inda suke mika irin nasu koke-koken da neman irin gudummawar da masarautar za ta iya bayarwa don ci gaban asibitin.

 

 

Sanarwar dakatar da bukukuwan sallah da masarautar ta fitar ya biyo bayan sanarwar da masarautar Zazzau karkashin Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna ta fitar da nata sanarwar na dakatar da bukukuwan sallah a masarautar.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.