Related Articles
Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina ya bayar da umarnin ci gaba da aiwatar da dokar hana fita a garuruwan Katsina, Batagarawa da Daura.
Kamar dai yadda aka Sani wadannan kananan hukumomi daman can suna cikin dokar hana fita lokaci mai tsawo domin yaki da cutar Covid – 19 da ale kira da Korona.
Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana wannan umarnin ci gaba da dokar ne a lokacin wani taron manema labarai da aka yi a gidansa Gwamnatin Jihar Katsina.
Gwamnan ya co gaba da cewa za a ci gaba da aiwatar da wannan dokar hana fita a wadannan kananan hukumomi guda uku domin rage walwalar Jama’a saboda sune keda kashi 80 na rahotannin samun mutane da wannan cuta a Jihar.
Masari ya ce kananan hukumomi 31 za a yi dokar yin amfani da Takunkumin rufe hanci da Baki, wanke hannu da abin wanke hannu da sauran yin aiki da dokokin kare kai daga wannan doka ta Korona bairus.
Da yake bayar da cikakken rahoton cutar a Jihar baki daya Gwamna Masari, karamar hukumar Katsina na da alkalumman da suka fi na ko’ina yawa da suka kai mutane 209 sai Daura mai mutane 79. Sai ya yi kira ga masu aikin bincike da su ci gaba da aiki tukuru yadda mutane za su zauna ba tare da daukar wannan cuta ta Covid – 19 da ake kira da Korona bairus.
Ya ce wannan saboda kula da al’adu da yanayin addini yake a tsakanin al’umma.
Gwamnan ya kuma yi magana game da halin tsaron da ake ciki a wadansu kananan hukumomi a Jihar, ya kuma taya al’ummar musulmi murnar kammala Azumin wannan shekarar.