Home / KUNGIYOYI / Masu Hali Su Rika Taimakawa Mabukata – Jagaban Matasa

Masu Hali Su Rika Taimakawa Mabukata – Jagaban Matasa

 

Ina son a kullum in ga jama’a a tare da ni
Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Abdullahi Idris da ake yi wa lakabi da Jagaban Matasa fitaccen dan siyasa ne a Jihar Kaduna ya jaddada kiran da yake yi wa daukacin al’umma Maza da Mata da su rika kula da taimakawa marasa karfin da suke tare da su.
Abdullahi Idris Jagaban Matasa ya yi wannan kiran ne Jim kadan bayan karbar lambar karramawa da ga kungiyar Mawallafa Jaridu da Mujallu mai suna “Arewa Publishers Forum”, da suka ba shi a garin Kaduna.
Abdullahi Jagaban Matasa ya ce hakika ya ji dadi kwarai da wannan karramawar da aka yi masa kasancewar an Zabo shi ne a cikin mutane da yawa amma aka Karrama shi da wannan lambar Yabo ta Mawallafa don haka wannan ba karamin abin alkairi ba ne a gare ni da duk wadanda suke tare da ni.
“Kasancewar ana cikin wani yanayi na rayuwa muna yin kira ga jama’a da su rungumi Akidar taimakawa Juna saboda yanayi na taimakekeniya na samar da ci gaban kowace irin al’umma, don haka duk dan abin da mutum ke ganin yana da shi ya taimakawa wanda bashi da hakan zai taimaka kwarai a samu Lada da kuma kyautata zumunci da kauna a tsakanin kowace irin al’umma da suka samu kansu a hali na zamantakewa”.
Abdullahi ya ce ” Koda siyasa ko ba siyasa mu jama’a ce abin alfahari mu kuma muna tare da su a koda yaushe Dare da rana safiya da maraice domin jama’a rahama ce”.
Tun da farko shugaban kungiyar Arewa Publishers Forum, Alhaji Sani Garba cewa ya yi babban dalilin da yasa suka Karrama Abdullahi Idris Jagaban Matasa shi ne irin yadda yake rungumar jama’a ta hanyar taimaka masu da jibintar al’amuran da ya shafi al’umma a koda yaushe.
” Mutum ne da koda yaushe zaka gan shi ya na tare da jama’a duk da irin wadatar da Allah ya bashi bai ta ba gudun jama’a ba, hakika a kan hakan muka ga ya cancanci wannan karramawar”.

About andiya

Check Also

Aliyu Sokoto tasks cabinet on transformation drive, ‘ be committed and sincere 

  By Suleiman Adamu, Sokoto SOKOTO state Governor Dr Ahmed Aliyu Sokoto has tasked members …

Leave a Reply

Your email address will not be published.