Home / Kasuwanci / Masu Sana’ar Sayar Da Mota Na Bukatar Tallafi – Na brazil

Masu Sana’ar Sayar Da Mota Na Bukatar Tallafi – Na brazil

 

Gwamnati Ta Bude Wa Masu Sana’ar Mota Wata Kafa Su Shigo Da Motoci

Mustapha Imrana Abdullahi

 

Shugaban Kungiyar masu sayar da motoci ta kasa reshen Jihar kaduna Alhaji Kwamared Ahmad Nabrazil ya yi kira ga Gwamnatin tarayyar Nijeriya da ta bude masu wata kafar da za ta ba su masu sana’ar mota wata kafar shigo da motoci ta kasa.

 

“Hakika Gwamnatin Nijeriya ta rufe wa masu sana’ar mota boda tun shekarar 2017 don haka muke murnar bude wannan boda da Gwamnati ta yi kuma muna fata lamarin bude bodar zai shafe mu”.

 

Saboda tun da aka rufe Bodojin Nijeriya aka hana shigowa da dukiyoyin masu sayar da mota ta kan iyakoki, amma a yanzu tun da har an bude muna fatar a saka da mu a ciki.

 

“Kuma ba munki Gwamnati ba ne, shi yasa muke rokon Gwamnatin ta san da mu ta bude mana wata kafa da zamu rika biyan harajin shigowa da motocin kasancewa kasa na bukatar kudi kuma mutanen da suke a kan iyakokin nan da masu hulda da su duk suna bukatar a bude domin suna samun Taro da Kwabo ta hakan wajen shigowa da motocin nan don haka in an bayar da wata kafa ga masu sana’ar mota za a samu albarka kwarai.

 

Saboda haka muke yin kira ga Gwamnati da kuma hukumar Kwastan da su kawo wadansu tsare tsaren da zai amfanar da kowa a kasa baki daya.

 

Muna kira ga shugabannin gidajen sayar da motoci da mabiyansu da su dukufa wajen yin addu’o’I kasancewar kasar na bukatar addu’a ne kwarai.

 

Kamar yadda aka san masu sana’ar sayar da motoci masu biyayya da’a da biyayya tare da yin kawaici, abin da duk Bana alkairi ba baka samun mai sana’ar mota na cikinsa a saboda haka muna yin addu’ar Allah ya kara mana ci gaba da zaman lafiya a kasa baki daya.

 

Muna fatar kada Allah ya mai maita mana irin wadansu matsalolin da suka faru a shekarar 2020 da ta gabata, kuma muna fatan dukkan Alkairan da suka faru a shekarar baya Allah ya ninninka mana su a wannan shekarar ya karo mana ci gaba.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.