Home / KUNGIYOYI / Matasan Arewa Sun Gargadi Gwamnonin Kudu Maso Gabas Game Da Kisan Yan Arewa A Yankin

Matasan Arewa Sun Gargadi Gwamnonin Kudu Maso Gabas Game Da Kisan Yan Arewa A Yankin

Kungiyar tuntuba ta matasan Arewa (AYCF) ta aikawa Gwamnonin yankin Kudu maso Gabas da game da KISAN da ake yi wa yan Arewa a yankin domin kawo karshen kisan mutanen da ba su ji ba – ba su ga ni – in ba haka ba su fuskanci ofishin hukuma.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin takardar bayanin bayan taron da suka gabatar a Kaduna, mai dauke da sa hannun shugaban AYCF na kasa Alhaji Yerima Shettima inda ya ce kisan da aka yi wa wasu yan Arewa a suke aiki ko saye da Sayarwa a yankin Kudu maso Gabas hakika ba abin da za a amince da shi ba ne kuma zai iya harzuka sauran mutanen yankin Arewa.
Sun ci gaba da bayanin cewa su na tsammanin Gwamnan Jihar Anambara Soludo ya yi amfani da kwarewarsa ta shugabanci wajen maganin kisan jama’a
“A batu na gaskiya Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas ne shugabannin tsaro na yankin, amma ba su yi komai ba domin tsayar da batun kisan mutanen Arewa a yankin na su, saboda haka ne muke ganin wannan al’amari ya zamo kisan kare dangi saboda haka mun yi Tir da lamarin, a dukkan yanayin da aka aikata shi da ake rabawa da sunan IPOB ko ESN”, kamar yadda aka bayyana a takardar bayan taron.
Kungiyar AYCF, a cikin takardar da ta rabawa jama’a cewa kisan da aka yi wa wata mata da yarta da kuma wani Kirista injiniyan Jirgin sama da ya kasance dan Arewa ne ya nuna a fili cewa rayuwar mutanen mu a yankin ba wani abu ba ce.
“Yin shuru da wadannan Gwamnonin suka yi duk da irin yadda aka kaiwa jama’a hari ga yayan mu maza da mata a yankin Kudu maso Gabas dole ne a hanzarta barinsa, sakamakon hakan muke aikawa da sakon gargadi kasancewar a Najeriya babu wata kabilar da ke da wani yancin tayar da tashin tashina kuma kasancewar mutanen Arewa masu girmama doka da ka’ida ba wai rauni ba ne”, inji AYCF daga yankin Arewa.

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.