Home / News / 2023: Ina Cikin Takara Ban Janye Wa Kowa Ba – Shadalafia

2023: Ina Cikin Takara Ban Janye Wa Kowa Ba – Shadalafia

Abdulwaheed O. Adubi, Kaduna
Dan majalisar dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar Kagarko, Honarabul Nuhu Goroh Shadalafia, ya Karyata jita- jitar da ake yadawa cewa wai ya janye wani na yin takarar dan majalisar dokoki na Jiha.
Ya bayyana batun jiga- jitar a matsayin aikin karya irin ta shedan, ya shawarci daukacin jama’a da kuma jam’iyya da su yi watsi da wannan bayanin mara tushe balantana makama.
Kamar yadda ya ce a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai a Kaduna a ranar Talata, ya shawarci daukacin al’umma da kada su amince da duk wani bayanin da ba daga gare shi ko shafinsa na facebook da whatsapp ba.
A cikin takardar, ya ci gaba da cewa, ” an jawo hankalinsa ne game da wannan kwaryar da ake yadawa a tsakanin jama’a musamman a mazaba ta cewa wai ni Honarabul dattijo Nuhu Machu Goroh Shadalafiya da ke takarar kujerar majalisar dokokin Jihar kafuna na janye takara ta wai ga wani mai su na Honarabul Ibrahim Simple Kogi domin zama dan majalisa”.
” Hakika wannan shiri ne kawai daga abokan adawar siyasa da ke ciki da wajen jam’iyyar APC da nufin karkatar da hankalin jama’a domin cimma wata biyan bukata kawai.
” Wadanda suke yawon yada wannan karyar shedanun su ne masu kudiri iron na shedan musamman game da ci gaba da kuma bunkasa Dimokuradiyya a mazabar mu. Saboda haka na Karyata wannan karyar kuma ba zan amince da hakan ba ga wasu su samu komai a cikin sauki a takara.
“Saboda haka nake kiran daukacin magoya baya na da su ci gaba da yin kokari har sai sun tabbatar da samun nasara an kunyata yan adawa”, tsohon mataimakin shugaban majalisar ya karfafa bayaninsa.
Idan zaku iya tunawa dan majalisa Shadalafia ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ne domin ci gaba da zama dan majalisar dokokin Jihar a satin da ya gabata.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.