Home / News / Matasan Arewa sun yi kira ga Gwamna Emmanuel ya fito takarar shugaban kasa a 2023

Matasan Arewa sun yi kira ga Gwamna Emmanuel ya fito takarar shugaban kasa a 2023

 

Gamayyar kungiyoyin ci gaban matasan Arewa a mahanga ta gaskiya da suka kunshi (Northern Youth for Good Governance da Arewa Political Awareness Initiative da Mufarka Arewa Youth Political Vanguard) sun bukaci Gwamnan Jihar Akwa Ibom Mista Udom Emmanuel da ya gaggauta bayyana fitowarsa takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ke tafe.

 

Babban sakataren kungiyar na kasa Bishir Dauda ne ya bayyana hakan a Abuja.

 

Magaji ya bayyana cewar a halin da ake ciki Najeriya na bukatar haziki, Jarumi kuma jajirtacce wanda zai ceto Najeriya daga halin da take ciki, a cewarsa ba kowa bane ya cancanci zama shugaban Najeriya na gaba kamar Gwamna Emmanuel na jihar Akwa Ibom.

 

“A halin da Najeriya take ciki yanzu, gibin da ke tsakanin masu mulki da wadan da ake mulka wagege ne, Najeriya na bukatar mutum mai kwazo da zai iya hade kan al’ummar Najeriya domin bayar da jagoranci na gari abin misali “.

 

“A matsayinsa na kwararre a kan harkokin tasarrufi da kudade, kuma Gwamnan da ya jagoranci jihar Akwa Ibom kuma ta samu ci gaba mai ma’ana, irin wannan mutum ne ya dace da shugabancin Najeriya a zabe na gaba mai zuwa.

 

“A saboda haka wannan gamayya ta kungiyoyin ci gaban matasan Arewa a mahanga ta gaskiya ta hanga ta hango Gwamna Udom Emmanuel a matsyin mafita ga Najeriya a shekarar 2023” a cewar Bishir Dauda.

About andiya

Check Also

Sokoto state government dethrones 15 traditional leaders, four others being investigated for various offences

  By S. Adamu, Sokoto Fifteen Sokoto traditional leaders have been dethroned by the Sokoto …

Leave a Reply

Your email address will not be published.