Home / Labarai / Matsalar Tsaro Na Hana Gwamna Matawalle Bacci – Dokta Sani

Matsalar Tsaro Na Hana Gwamna Matawalle Bacci – Dokta Sani

Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban Kwamitin tsaro a Jihar Zamfara Dokta Sani Abdullahi Shinkafi Wambai, ya bayyana cewa matsalar tsaron da Jihar Zamfara ke fama da shi na hana Gwamna Muhammad Bello Matawalle Bacci saboda da tsananin damuwar da yake yi game da lamarin.
Dokta Sani Abdullahi ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taron yan asalin karamar hukumar Shinkafi, karkashin kungiyar ci gaban al’ummarsu baki daya mai suna “SEDA” taron dai an yi shi ne a garin Kaduna.
Dokta Sani Wambai, ya ci gaba da cewa akwai wadansu abubuwan da jama’a ba su Sani ba da dama da ke faruwa game da matsalar tsaron Jihar Zamfara, wanda jama’a ne da kansu ya dace su tashi tsaye domin ganin an samu maslaharsu, amma sai a rika tunani na daban.
Sani ya kara da cewa suk masu zargin Gwamnati game da wannan batu na tsaro hakika suna yin babban kuskure domin ba ruwan Gwamnati a cikin wannan lamarin,matsala dai ce da ke cikin al’umma don haka ya zama wajibi ga jama’a su tabbatar sun bayar da dukkan gudunmawar da ya dace wajen ganin an magance matsalolin tsaro ta yadda kowa zai amfana.
“A matsayin da nake ciki na san cewar Gwamnati na iyakar bakin kokarinta wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al’umma amma wadansu mutanen da ba su san yadda lamarin yake ba, su na yin wani tunani can daban”, inji shi.
Dokta Sani Wambai ya kuma lissafa wa mahalarta wannan taron da kungiyar SEDA ta kira wadansu daga cikin matsalolin da tsaro musamman ta fuskar kokarin kawar da yan bindiga ke tattare da su da ya bayyana cewa sun hada da tsarin mu’amallar kudi na POS da wasu batagari ke amfani da shi wajen hada hadar kudin yan bindiga, inda ake wuce ka’idar yin amfani da POS din.
Saboda haka wannan matsala ta POS ta zama wata babbar matsalar da ke kawo cikas wajen samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Sani Wambai ya ce dole sai shugabannin addini sun tashi tsaye wajen fadakar da jama’a saboda akwai wani Limamin da ke tare da wadannan mutane yan bindiga, akwai kuma wadansu malamai da ke aikin ba yan bindigar nan sa’a domin su gudanar da miyagun  ayyukansu wanda yin hakan ba dai – dai ba ne.
Ya kuma bayar da misalai inda ya ce akwai wadansu wurare da bayanai suka tabbatar da cewa yan bindiga na shigowa su na sagewa cikin al’umma don haka sai jama’ar wurin sun raba kansu da duk wani batagari.
Dokta Sani Wambai ya kara da cewa akwai wata matsalar da ke addabar al’umma ita ce ta yin ta’ammali da miyagun kwayoyi, “akwai wata kwayar da ake kira kirak wadda duk wanda ya sha ta zai iya ganin cewa shi babu abin da ba zai iya runguma ba domin duk wata na’tsuwa da sanin abin da yakamata duk an cire masa shi zai ga komai zai iya aikata wa a matsayin dai- dai don haka abin da zai aikata sun hada da kai wa jama’a hari ba su ji ba ba su gani ba”.
Ya kuma yi bayanin wadansu wuraren da batagari ke taruwa suna holewarsu da Gwamnati ta dauki mataki, don haka sai jama’a sun tashi tsaye sun kawar da wadannan abubuwa da nufin samun zaman lafiya.
Mahalarta taron dai da suka zo daga karamar hukumar Shinkafi sun yi jawabai da kuma tambayoyi da dama, kuma shugaban kwamitin tsaro Dokta Sani Abdullahi Wambai, ya yi cikakkun bayanai da suka gamsar da al’umma abin da wasu da dama ke cewa ai ba su Sani ba cewa ba laifin Gwamnati ba ne, hakika matsalar tsaron nan na cikin jama’a domin wasu batagari ne ke aikata su da kansu.
Dokta Sani ya ci gaba da cewa kuskure ne wasu su rika ganin cewa an bar karamar hukumar Shinkafi a baya, domin Gwamnati ta aiwatar da dimbin ayyukan raya kasa wasu kuma ana kan kokarin fara aiwatar da su duk saboda mutanen karamar hukumar Shinkafi da Nijeriya baki daya su samu romon Dimokuradiyya.
Sai kuma wata babbar matsalar da ta fi kowace girma ita ce ta masu bayar da bayanai ga yan bindiga wanda Dokta Sani Wambai, ya fayyace wa jama’a cewa daga cikin matsalolin ita ce gagarumar matsalar da ta fi kowace zama mai illa ga Gwamnati, jami’an tsaro da jama’a baki daya, kuma masu aikata hakan su na nan cikin jama’a.
Don haka kada a mance cewa matsalar tsaro na cikin al’umma saboda haka sai an hada hannu wuri daya baki daya a dauki matakan magance matsalar.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.