Home / Labarai / Yin Aikin Ba Sani Ba Sabo Zai Magance Matsalar Tsaron Jihar Zamfara

Yin Aikin Ba Sani Ba Sabo Zai Magance Matsalar Tsaron Jihar Zamfara

Mustapha Imrana Abdullahi
Wani fitaccen mai fafutukar kare hakkin jama’a Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya bayyana daukar matakin aikin ba Sani ba sabo a matsayin abin da ya dace domin magance matsalolin tsaron da ke addabar Jihar.
Gwamnati na aiki amma matsalar masu bayar da bayanan sirri ga yan bindiga ne matsalar da ake fama da ita a Jihar Zamfara don haka a hanzarta magance ta ta yadda za a samu nasarar da kowa ke bukata.
“Musamman mu a karamar hukumar Shinkafi matsalar masu bayar da bayanan sirri ga yan bindiga wato (Infoma) ce matsalar da ke addabar karamar hukumar Shinkafi, saboda haka ya dace Gwamnati ta dauki matakan da ya dace domin magance wannan matsalar da ke addabar yankin arewacin Najeriya.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, a wajen babban taron da al’ummar Shinkafi domin tattauna hanyoyin warware matsalolin tsaron da suka addabi karamar hukumar Shinkafi da Jihar Zamfara baki daya da aka yi a garin Kaduna.
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya ce a matsayinsu na yan asalin Jihar Zamfara daga karamar hukumar Shinkafi su na sane da irin kokarin da Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Dokta Muhammad Bello Matawalle ke yi wajen kokarin inganta al’amuran tsaro domin jin dadin jama’a.
“Na gano cewa dukkan matsalolin tsaron da ake fuskanta danga ne da tsaro ba laifin Gwamnati ba ne mun gano cewa laifin jama’a ne kawai don haka sai jama’ar sun dai- daita kawunansu ta yadda harkar tsaron za ta inganta kowa ya amfana”, inji Dokta Suleiman.
Dokta Shinkafi ya ci gaba da cewa shi a matsayinsa ya na bayar da shawara cewa a kama dukkan wani mai hannu a cikin batun bayar da bayanai ga yan bindiga da ake kira Infoma domin suna mayar da hannun agogo baya.
A wajen taron dai da aka yi a Kaduna ya samu halartar dukkan masu ruwa da tsaki na yan asalin karamar hukumar Shinkafi, wanda wadansu ma da ba su samu damar halartar wannan taro ba duk an tattauna da su ta hanyar sadarwar yanar Gizo kuma duk sun bayar da ta su gudunmawar.
Dokta Shinkafi ya ci gaba da cewa babban taron ya yanke hukuncin cewa dukkan masu wannan aika aikar bayar da bayanan sirri ga yan bindiga a mika sunayensu ga Gwamnati domin ta dauki matakin da ya dace.
“Za kuma mu dauki karin masu aikin sa kai ban da na Gwamnati wanda ta yi alkawarin za ta dauka, mu ma mun cimma matsayar kara daukar masu aikin sa kai domin karin tabbatar da tsaro a karamar hukumar Shinkafi.
Mun kuma tattauna irin yadda Gwamnati ta dauki matakai kuma an samu ci gaba kwarai, saboda Gwamnati duk iyakar kokari Gwamnatin na daukar mataki kuma ana samun nasara sai dai idan Gwamnatin ta dauki mataki sai wasu su rika warware irin tukkar da Gwamnatin ke yi.
Sai dai akwai matsalar makiya masu aikin kiyayya da ke neman su hada mu, amma tun da mun gane to, zamu ci gaba da jajircewa wajen bayar da hadin kai da dukkan goyon baya ga Gwamnati domin a samu nasarar da ta dace.
Muna kira ga Gwamnati da ta kama dukkan masu aikin bayar da bayanan sirri ga yan bindiga domin hukunta su dai- dai da aikin da suka aikata wajen lalata harkokin tsaro, wanda hakan ya haifar da matsaloli da dama.

About andiya

Check Also

Northern Christian Leaders Pay Homage to Khalifah Sanusi, Strengthening Ties.

Northern Nigerian Christian Clerics Pay Homage to His Highness Khalifah Sanusi Lamido Sanusi to Strengthen …

Leave a Reply

Your email address will not be published.