Home / KUNGIYOYI / MU NA BUKATAR DAN TAKARAR GWAMNAN KADUNA DAGA SHIYYA TA DAYA – YAN APC

MU NA BUKATAR DAN TAKARAR GWAMNAN KADUNA DAGA SHIYYA TA DAYA – YAN APC

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
WADANSU matasa daga cikin jam’iyyar APC a Jihar Kaduna sun bayyana kudirinsu na ganin dan takarar jam’iyyar APC na Gwamna ya fito daga shiyya ta daya.
A ta bakin mai magana da yawunsu Dokta Ahmad Usman Dan Baba, sun shaidawa manema labarai a Kaduna cewa sun dauki wannan mataki ne sakamakon irin yadda yankin ya dade ya na bayar da gagarumar gudunmawa wajen samun nasarar APC a dukkan zaben da ya gabata.
“Mun kuma kara bayar da gudunmawa a lokacin babban zaben da ya gabata inda yankin
“Hakika muna godiya bisa irin yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ke yin ayyuka a ko’ina a duk fadin Jihar Kaduna da nufin kara inganta rayuwar al’umma baki daya, kuma hakan duk ya samu ne sakamakon irin cikakken hadin kai da goyon bayan da mutanen yankin shiyya ta daya suka dade su na bayarwa ga tafiyar wannan Gwamnatin APC”.
Sun kara da cewa da akwai wadansu kujerun yan majalisarwakilai  baki daya na APC ne a wannan yankin na shiyya ta daya, kuma a kujerun yan majalisar dokokin Jihar Kaduna nan ma daya ce ba ta APC ba haka batun yake a wajen shugabannin Kananan hukumomi daya ce kawai ita ma mun san yadda aka yi sakamakon tsamin dangantaka da aka samu ne ya haifar da hakan don haka a wannan karon kujerar Gwamnan Jihar Kaduna daga yankin Shiyya ta daya ne kawai dacewar abin da fatan dukkan wadanda suka kasance masu ruwa da tsaki a lamarin za su yi aiki kan jiki kan karfi lamarin ya tabbata wanda hakan shi ne adalci.
Kuma sun kara da fayyace cewa su na sa ne fa yawan kuri’un da ake samu daga wasu yankuna a jam’iyyar APC raguwa kawai yake yi a koda yaushe, ” Amma yawan kuri’un da APC ke samu a yankin shiyya ta daya karuwa kawai abin yake kuma hakan a bayya ne yake, har ma karamar hukumar Zariya ita ta fi kowace karamar hukuma a Najeriya ba shugaba Bubari kuri’a a zaben da ya gabata ga dai misalai nan da yawa na cancantar kujerar Gwamna a APC sai shiyya ta daya”.
Masu tambaya na cewa shin ina kujerun Gwamnan Kaduna, Kujerar mataimakiyar Gwamna,Kakakin majalisar dokokin Jiha, wace shiyya ke da kujerun ministoci guda biyu daga Jihar Kaduna ai duk ba daga shiyya ta daya ba ne,kuma mutanen shiyya ta daya ke kafa Gwamnatin domin kuri’unsu ne masu yawa”, inji yayan APC a Jihar kaduna.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.