Home / Kasuwanci / Muna Bukatar Taimakon Gwamnati Da Kanfanonin Samar Da Kayan Shayi – Kungiyar Yan Shayi

Muna Bukatar Taimakon Gwamnati Da Kanfanonin Samar Da Kayan Shayi – Kungiyar Yan Shayi

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

Malam Aliyu Yahaya shugaba ne na kungiyar masu sana’ar sayar da shayi ta kasa reshen Jihar Kaduna ya yi kira ga daukacin fallayen Gwannati guda Uku da ake da su a Najeriya da su rika bayar da tallafi ga masu sayar da shayi da ke sako da Lungun kasar.

“Kamar ni na yi shekaru 47 ina sana’ar sayar da shayi kuma ni, ina nan cikin garin Kaduna ne na samu nasarar koyawa mutane da dama wannan sana’a ta sayar da shayi. Kuma ina tabbatarwa da Gwamnati cewa babu wani mai sana’ar sayar da shayi da bashi da a kalla mutane uku ko biyu a karkashinsa”, inji shugaban Yan Shayi.

Ya dai bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a garin Kaduna.

Aliyu Yahaya ya ci gaba da bayanin cewa kamar yadda suke yin kira ga Gwamnati a Najeriya haka suke yin kira kuma ga wasu kamfanonin da suke yin kayan abincin  da masu sayar da shayi ke saye suna yin amfani da su wajen sana’ar su da su hanzarta duba hanyoyin da za su taimakawa yayan kungiyar domin dorewar sana’ar. Saboda haka muke yin kira ga kamfanonin nan da su duba hanyoyin da za su taimakawa yayan kungiyar masu sana’ar sayar da shayi, wanda idan an yi hakan za a taimakawa dimbin jama’ar kasa baki daya”.

Aliyu ya kara da cewa kamar yadda Allah ya taimaka masa har ya samu shekaru 47 ya na sana’ar sayar da shayi ya samu nasarori kwarai a kan wannan sana’ar domin muhimmancin ta.

” Wadannan kamfanonin da muke magana a kansu sun hada da kamfanin Madara, Sukari, Naskofi, Burodi da dai sauran kamfanonin da ke yin kayan da ake hada shayi da su, saboda a halin yanzu yayan kungiyar masu sana’ar shayi na bukatar a taimaka masu domin al’umma su samu saukin abincin da suke yin amfani da shi da suka hada da shayi, taliyar Indomi, Kwai da Burodi a wasu wuraren ma har da masu hada wa da Nama, Kifi da Dankalin Turawa da dai sauran kayan hadin Shayi.

Malam Aliyu ya ci gaba da bayanin cewa cire tallafin mai ya shafi harkarsu da sana’ar Shayi da lamarin a yanzu ya haifarwa da yayansu jinjiki kwarai da gaske don haka ne za mu yi babban taro na kasa domin a tattauna hali da yanayin da masu sana’ar yin Shayi ke ciki a dukkan fadin kasa baki daya, sai a san matsayar da za a dauka.

” Da yawa wadansu masu Shayi na rufewa sakamakon tsadar kayan hadin Shayin da ake fama da ita, saboda da yawa wasu masu Shayin ba su san abin da suke yi ba a game da batun Ruwan Shayin da suke Sayarwa ba domin Mai Shayi ne zai iya kashe a kalla naira dubu Uku ya hada Shayi amma bai san ko Kofi nawa ba ne a cikin garwar Shayin da ya ke da ita ba,Musamman ta yadda idan an yi kiyasin Sayarwa misali naira Talatin Talatin kudinsa ya dawo ko yaya mafi yawansu ba su san hakan ba domin babu kididdiga a kan hakan”.

Ya kuma tabbatarwa da yayan kungiyar cewa nan gaba har taron bita ma za a yi wa masu sana’ar domin kowa ya san abin da ya dace ya Sani su sayar da Shayi ko an kara kudi ko su kara ko su bar shi a hakan ne.

Shekaru 47 da na yi ina sana’ar sayar da Shayi duk abin da Shayi keyi hakika ya yi Mani, kuma a halin yanzu idan naje wajen mai sayar da Shayi na ce masa ba ni Shayi kudin da zai gaya Mani idan ya na samun wani abu lallai zan Sani idan kuma baya samu ma na Sani domin Shayi na tafiya da Buredi ne, amma sakamakon tsadar kayan ya Sanya wadansu a yanzu zuwa suke yi kawai su sayi Shayin ba tare da Biredi ba don haka muna neman taimakon Gwamnati da Kamfanonin yin kayan hada Shayi duk da nufin jama’a su samu sauki kawai.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.