Home / Big News / Muna Da Makarantar Koyar Da Marayu Kyauta A Kaduna – Abdul’azeez Kaka

Muna Da Makarantar Koyar Da Marayu Kyauta A Kaduna – Abdul’azeez Kaka

Daga Imrana Abdullahi
Abdul’azeez Abubakar da ake yi wa lakabi da Kaka, dan takarar majalisar Wakilai domin wakiltar al’ummar Karamar hukumar Kaduna ta Arewa ya bayyana cewa yaye daliban da aka yi wadanda suka haddace littafin Allah Alkur’ani mai girma abin a yaba ne ga wadanda suka yi wannan gagarumin aikin karantar da daliban.
Abdul’azeez Abubakar Kaka ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron saukar yayen dalibai mahaddata Alkur’ani da makarantar Daru Sigaril HUFFAZ ta yi a dandalin tunawa da Murtala a Kaduna.
“Abu ne abin ban sha’awa a samu yan shekaru Bakwai zuwa Takwas sun haddace Kur’ani abu ne abin ban sha’awa kwarai da gaske, samun hakan alama ce da ke cewa lallai Kur’ani na nan kuma gaba za ta yi kyau ga yara, kuma na ji dadi da aka yi kira ga iyaye cewa a mayar da yara makaranta hakan ma ya na da kyau kwarai.
“Muma muna da wata makarantar da ake taimakawa marayu ana ba su ingantaccen ilimin addinin Musulunci da Boko kuma a kyauta muke yin wannan kokarin gina al’umma ta gari kuma irin wannan lamarin na yi. mana dadi duk inda aka gayyace mu muna zuwa wurin domin girmama Alkur’ani mai tsarki
Abdul’azeez Kaka, ya kuma sha alwashin cewa idan Allah ya bashi damar zama dan majalisar wakilai ta kasa zai yi dukkan mai yiwuwa domin ganin ya nemowa jama’ar karamar hukumar Kaduna ta Arewa abin da ya dace su samu na romon dimokuraɗiyyar.
“Ko a yanzu da ma ba zababbu ba amma mun yi abubuwan ci gaban jama’a da yawa da suka hada da makarantu da sauransu duk domin jama’a su amfana mu kuma mu kwashi Lada mai yawa daga Allah subhanahu wata’ala. Saboda haka ne muke shaidawa da jama’a cewa idan mun samu wannan nasarar zama dan majalisar tarayya za mu yi abin da ya wuce wanda muka yi a halin yanzu, domin za mu kara inganta ilimin addini, Boko da kuma ilimin koyon sana’o’i, yadda yaro zai ce makaranta kuma ya rika koyon sana’a har ya samu abin da zai rika yi wa iyayen sa cefane”, inji Kaka.

About andiya

Check Also

Dangote, Pope Leo XIV, Trump, Xi Jinping, others Named in TIME 100 Most Influential People for 2026

  Renowned African industrialist and philanthropist, Aliko Dangote, has been named among TIME Magazine’s 100 …

Leave a Reply

Your email address will not be published.